Tura ta kai bango: Za mu yi amfani da 'tsafi' mu fito da Sunday Igboho daga gidan yari, Ƙungiyar Agbekoya
- Wata kungiyar manoma mai suna Agbekoya Farmers Society of Nigeria ta bayyana cewa za ta yi amfani da tsafi ta fito da Sunday Igboho daga gidan yari
- Kamorudeen Okikiola, shugaban kungiyar ya ce Igboho ba mai laifi bane, kawai gwamnatin Najeriya ce ta hada baki da gwamnatin Jamhuriyar Benin don tsare shi
- Kungiyar ta yi zanga-zanga na lumana don neman a saki Igboho, inda daga baya bisani suka yi tattaki zuwa gidan basarake suka mika masa wasika na bukatun da suke so daga Shugaba Buhari
Osun - Kungiyar manoma ta Agbekoya a Najeriya ta bayyana cewa za ta yi amfani da 'tsafi' ta ceto mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo aka Sunday Igboho idan gwamnatin Jamhuriyar Benin ta cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
Kamorudeen Okikiola, shugaban kungiyar ya ce Igboho ba mai laifi bane, amma mai neman 'yanci ne da aka tsare shi ba bisa ka'ida ba da hadin bakin gwamnatin Najeriya, rahoton Vanguard ta ruwaito
Ya yi wannan jawabin ne yayin wata tattaki na zaman lafiya da aka yi a Osogbo, babban birnin Jihar Osun a ranar Alhamis.
Ya ce:
"Sunday Igboho ba mai laifi bane kuma mun san ana tsare da shi ba bisa ka'ida bane, Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta dena kai shi kotu, don haka, muna son a sake shi ta hanyar kotu, idan ba su sake shi ba, za mu yi amfani da tsafi mu fito da shi. Na maimaita, mu Agbekoya, za mu fito da shi daga Jamhuriyar Benin mu dawo da shi gida."
A kan halin da Najeriya ke ciki, Okikiola ya yi kira da cewa a koma tsarin da ake amfani da shi a 1960 ko a sauya tsarin kasar kafin zaben 2023, yana mai cewa hakan ne zai kawo cigaba a kasar.
Ya koka kan karuwar rashin tsaro a Najeriya, yana mai gargadin cewa yan siyasa za su gane kurensu idan suka cigaba da wasa da hankalin talakawa.
Okikiola ya kuma yi kira da cewa ya kamata Najeriya ta mayarwa sarakunan gargajiya ayyukansu a wani mataki na dawo da tsaro a kauyuka, Vangaurd ta ruwaito.
Masu zanga-zangan sun hadu a Olaitan daga nan zuwa bi ta Odi-Olowo, Asubiaro, Isale-Osun, Idi-Omo zuwa Ataoja daga karshe suka tsaya a fadar Oba Jimoh Olaonipekun suka mika masa wasikar da ke dauke da bukatun da suke su Shugaba Buhari ya musu.
Gwamnatin Buhari na kitsa yadda za ta kashe ni, Sunday Igboho
A baya, Sunday Igboho, ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya na shirin halaka shi a kasar Jamhuriyar Nijar, Vanguard ta ruwaito.
Idan ba a manta ba jami’an tsaron Brigade Criminelle sun kama Igboho a ranar 19 ga watan Yulin a Kwatano. Duk da duk kokarin da aka yi don sakinsa abin ya ci tura don ya kwashe kwana 161 a hannunsu.
Olayomi Koiki, Kakakin Igboho, a wata murya da ya saki a ranar Talata da yamma, ya zargi shugaban kasa Patrice Talon na Jamhuriyar Benin da aiki da Gwamnatin Najeriya wurin ganin sun dawo da Igboho Najeriya.
Asali: Legit.ng