Tashin hankali: Ɗan acaɓa ya kashe abokin aikinsa yayin dambe a wurin cin shinkafa
- Wani dan acaba yana hannun hukuma bayan ya halaka abokin sana’arsa wani wurin siyan abinci a Jihar Abia kuma a bainar jama’a
- Lamarin ya auku ne a layin Uzompka da ke anguwar Amaiyi a yankin Owerri-Aba cikin karamar hukumar Ugwunagbo ranar Litinin
- Wani ganau ya shaida yadda makashin ya je siyan abinci inda ya bukaci mai sayar da abinci ta dakata da zuba wa kowa sai shi
Jihar Abia - Wani dan acaba yana hannun jami’an tsaro bayan ya halaka abokin sana’arsa a wani wurin cin abinci da ke Jihar Abia, The Nation ta ruwaito.
Lamarin ya auku ne a layin Uzompka da ke anguwar Amaiyi a yankin Owerri-Aba a cikin karamar hukumar Ugwunagba a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu.
Mamacin bai dade da shiga wurin cin abinci wanda aka sa wa suna Nwanyi Mmonghon tare da wani Chinenye ba aka halaka shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani ganau ya yi bayani dalla-dalla akan tushen rikicin
Wani ganau ya bayyana cewa:
“Wani dan acaba, Oberagu da ke zaune a wurin cin abinci, wanda ya isa wurin kafin Chinenye ya bukaci ya tsaya a gama sallamar su.
“Mai sayar da abincin ta goya masa baya inda taje zubo wa wadanda suka je siyan abincin kafin Chinenye.
“Bayan nan ne Chinenye ya fara yi wa mutana barazanar zai halaka su yana hargagi da cewa matsawar matar ta fara zuba wani sai ya lalata wurin.”
The Nation ta ruwaito yadda ganau din ya kara da cewa wannan babatun da Chinenye ya yi shi ne ya hassala sauran ‘yan acaba inda suka taru suka lakada masa na jaki.
A cewar ganau din, yayin da suke ci gaba da cin abinci sai ga Chinenye tare da wasu ‘yan acaba wanda akan yasa kowa ya tsere, daga nan Chinenye ya janyo dan acaban ya harbe shi a ciki sannan suka tsere.
Bayan kai shi asibiti likitoci suka bayyana cewa ya mutu
An yi gaggawar kai dan acaban asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.
Mutuwarsa ta janyo gagarumin tashin hankali a garin don ‘yan uwansa sun dinga sanya wa gidajen ‘yan uwan wanda ake zargin ya halaka shi wuta.
Da farko Chinenye ya gudu ne, amma daga baya ya kai kansa ofishin ‘yan sanda da ke Ugwunagbo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya mika kansa ga hukuma.
Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta
A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alawadai akan kona gonarsa da wasu batagari suka yi a garin Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Kudu a Jihar Binuwai a kwanakin karshen makon nan, The Punch ta ruwaito.
Tsohon shugaban kasar mai shekaru 84 ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan abu kuma ya ce sai jami’an tsaro sun gano wadanda suka tafka ta’asar.
The Punch ta ruwaito yadda batagari suka babbake gonar Orchard wacce mallakin babban mutumin ne na Hilltop da ke Abeokuta a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng