Gwamnati ta yadda ana cikin matsala bayan hango tulin bashin da ke wuyan Najeriya
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya koka a kan bashin da Najeriya take biya
- Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya ce abin da gwamnati ke batarwa wajen biyan bashi ya kai $4tr
- A wajen wani taro Lawan ya zargi kungiyoyin haraji da hannu wajen sukurkucewar tattalin arziki
Abuja - A wajen wani taro na CITN, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da cewa akwai bashi mai yawa a kan gwamnatin tarayya.
Jaridar Sun News ta rahoto Sanata Ahmad Ibrahim Lawan yana cewa bashin da Najeriya ke biya ya karu daga Dala tiriliyan 2.5 a 2019 zuwa Dala tiriliyan 4.1 a yau.
Shugaban majalisar dattawan ya yi jawabi na musamman yayin da kungiyar kwararrun malaman haraji watau CITN ta ke bikin cika shekaru 40 da kafuwa.
Ahmad Ibrahim Lawan ya ce an samu karin Dala tiriliyan 1.6 a abin da gwamnati take kashewa wajen biyan bashi. An samu wannan kari a cikin kusan shekara biyu.
Abin da hukumomin karbar haraji da nemawa gwamnatin tarayya kudin shiga suka iya tatsowa a shekarar 2020 bai wuce Dala tiriliyan 8 ba a cewar Sanata Lawan.
Nazif Abdullahi Darma ya wakilci Lawan
Farfesa Nazif Abdullahi Darma mai taimakawa shugaban majalisar wajen harkar tattalin arziki shi ne ya wakilce shi a wajen wannan biki da aka shirya a garin Abuja.
A madadin Lawan, Farfesa Nazif Darma ya fito karara ya zargi kungiyar CITN da taimakawa wajen tabarbarewar tattalin arziki, ya ce ba za a ce babu hannunsu ba.
“A shekarar bara bashin da ake biya ya kai $11. 93tr. A yau mu na da gibin kusan Dala biliyan 500 na gina abubuwan more rayuwa.”
“Kasar nan ba za ta shiga cikin wannan matsala ba idan ba tare da sa hannun manya irinsu CITN da sauran kungiyoyin ma’aikata ba.”
- Farfesa Nazif Abdullahi Darma
Farfesan ya ke cewa duk shekara sai an samu karin mutane kimanin miliyan shida a Najeriya, a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar yake motsawa da kasa da 4%.
Sauran wadanda suka samu halarta kuma suka yi jawabi a wajen taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ta bakin Zainab Shamsuna Ahmed.
Sababbin nadin mukami
A ranar Laraba ne ake jin Fadar shugaban kasa ta aikawa majalisar dattawa takarda ta na neman a nada kwamishinoni a hukumar NERC mai kula da wutar lantarki.
Mai girma Muhammadu Buhari ya kuma nada Darekoci a Hukumomin Nigerian Midstrea & Downstream Petroleum Regulatory Authority dahukumar nan ta NDIC.
Asali: Legit.ng