Hushpuppi: Kotun Amurka ta dage ranar yanke wa kasurgumin dan damfara hukunci
- Wata kotun kasar Amurka da ke zama a birnin California ta sanar da dage ranar yanke wa gagarumin dan damfara Hushpuppi hukunci
- Kamar yadda alkalin kotun, Otis D. Wright ya bayyana cewa, za a yanke hukuncin a ranar 11 ga watan Yulin shekarar nan
- Da farko za a yanke wa Ramon Abbas wanda ya amsa laifin damfarar makuden daloli da ake zarginsa da yi a ranar 14 ga watan Fabrairu
Wata kotu da ke zama a birnin California ta dage ranar yanke wa gagarumin dan damfarar nan da ya yi tashe a kafar sada zumunta, mai suna Ramon Abbass amma aka fi sanin sa da Hushpuppi hukunci kan damfarar makuden kudi daga mutane daban-daban.
Kotun kasar Amurkan ta dage zaman yanke hukuncin zuwa ranar 11 ga watan Yuli mai zuwa, akasin ranar Juma'a 14 ga watan Fabrairun da aka sanya a baya, aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Maganar kashe Hanifa ta shiga majalisar wakilai, an caccaka tsinke kan nema mata adalci

Source: Instagram
Kotun ta bayar da wannan sanarwan ne a ranar 2 ga watan Fabrairun 2022 inda tace:
"Duba da bukatar lauyoyi, a dage yanke hukuncin har zuwa ranar 11 ga watan Yulin shekarar nan da misalin karfe 11 na safe."
A bayan kotun ta sanar da cewa za ta yanke wa Abbass wanda ya amsa tuhumar da ake masa ta damfarar mutane miliyoyin daloli a kasashen duniya daban-daban.
Mai shari'a Otis D. Wright, alkalin kotun ya kara da bayar da umarnin a cigaba da garkame dan damfarar har zuwa lokacin yanke hukuncin.
Mun kammala bincike a kan Abba Kyari - Shugaban ‘Yan Sanda ya fadi abin da ake jira
A wani labari na daban, shugaban ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya yi magana game da rade-radin cewa Amurka ta bukaci a mika mata Abba Kyari.

Kara karanta wannan
Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 28 ga watan Oktoba, 2021, inda aka ji Usman Alkali Baba yana cewa bai san da maganar nan ba.
IGP Alkali Baba yace sam bai da labarin hukumomin kasar Amurka sun gabatar da takarda, suna neman a mika masu jami’in ‘dan sandan Najeriyar.
Hakan na zuwa ne bayan an yi ta jita-jita cewa hukumar FBI mai bincike a Amurka ta nemi a damka mata DCP Abba Kyari da nufin a bincike shi.
Asali: Legit.ng