Jami'an Kwastam sun yi ram da manyan motoci 17 maƙare da buhunan Shinkafar kasar waje
- Hukumar kwastam ta samu nasarar kama manyan motocin dakon kaya 17 maƙare da buhunan shinkafar waje a Ogun
- Mukaddashin kwanturolan sashin yaƙi da fasa kwauri a shiyyar A, Hussein Ejibunu, yace jami'an sun kwato makudan kuɗaɗen haraji
- Yace jami'ai za su ƙara zage dantse a wannan shekarar saboda sun samu sabbin kayan aiki
Ogun - Jami'an hukumar kwastam na sashin Operation a shiyyar A, ranar Laraba, sun sanar da kwace manyan motocin dakon kaya 17 maƙare da Shinkafar waje ana kokarin shigo da ita cikin Najeriya.
Tribune Online ta rahoto cewa jami'an sun yi ram da manyam motocin dakon kayan ne a yankin Papalanto a jihar Ogun.
Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a Legas, muƙaddashin Kwanturola na shiyyar, Hussein Ejibunu, ya bayyana yawan shinkafar da suka kwace cikin makonni biyar kacal.
A cewarsa, jami'ai sun yi ram da buhunan Shinkafa 9,697 mai nauyin kilo 50, Katan-Katan na Shinkafar Basmati mai nauyin kilo 5, da kuma Buhuna masu nauyin kilo 25 guda 297.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Vanguard ta rahoto Yace:
"Jami'an sashin Operation na shiyya ta A a hukumar NCS ta cigaba da aikinta na yaƙi da fasa kwaurin kayayyaki a watan Janairun 2022."
"Mun kwace kaya da suka kai darajar biliyan N4.6 kuma mun tattara zunzurutun kuɗi da suka kai miliyan N192m a matsayin haraji."
Shin sun kama yan fasa Kwauri?
Muƙaddashin Kwanturolan yankin ya ƙara da cewa jami'an sun cafke mutum 23 da ake zargin suna da hannu a fasa kwaurin kayayyaki.
Ya jaddada cewa jami'an dake sashin yaƙi da fasa Kwaurin kayayyaki ba bisa ƙa'ida ba za su ƙara zage dantse a sabuwar shekara saboda kayan aikin da gwamnati ta samar musu.
A wani labarin na daban kuma Halin da ake cikin kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace
A watan da ya gabata ne wasu miyagun yan bindiga suka yi garkuwa da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan a Bayelsa.
Sama da mako ɗaya da faruwar lamarin, wata majiya daga cikin iyalansa ta shaida cewa har yanzun maharan ba su tuntuɓe su ba.
Asali: Legit.ng