NNPC za ta fitar da Najeriya daga cikin talaucin makamashi cikin shekaru 4, GMD Mele Kyari

NNPC za ta fitar da Najeriya daga cikin talaucin makamashi cikin shekaru 4, GMD Mele Kyari

  • Jami'ar FUTMinna ta karrama Mallam Mele Kyari da digirin doktora bisa kokarin da yake yiwa Najeriya
  • Mallam Kyari ya bayyana cewa rabin gidajen Najeriya na fama da rashin wutan lantarki
  • Kamfanin NNPC ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar cire tallafin man fetur gaba daya

Dirakta Manajan kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa bisa ayyukan da sukeyi a masana'antar mai da iskar gas, Najeriya zata fito daga halin talaucin makamashi cikin shekaru hudu.

GMD Mele Kyari
NNPC za ta fitar da Najeriya daga cikin talaucin makamashi cikin shekaru 4, GMD Mele Kyari Hoto: NNPC
Asali: Facebook

Kyari ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda jami'ar fasahar tarayya dake Minna FUTMinna ta karramar da difirin doktora, rahoton AriseNews.

Yace:

"Hanya daya da kamfanin nan zai yiwa yan Najeriya aiki shine fada musu gaskiya da kuma sanar da su muna dukkan abinda zamu iya wajen tabbatar da kamfanin ta inganta kasa."

Kara karanta wannan

Tafiya a mota: Gwamna ya makale a hanyar Kaduna, jirgi ya dauke shi cikin gaggawa

"Kun san makamashi shine komai. Babu kasar da zata samu cigaban tattalin arziki ba tare da makamashi ba."
"A yau, akwai talaucin makamashi, kuma kashi 50 na yan Najeriya ba su da lantarki. Amma za'a iya sauya wannan saboda muna da arzikin makamashi kuma muna gina abubuwan da cikin shekaru uku zuwa hudu, kasar nan za ta fita daga kangin talauci."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng