Buhari ya bada izinin fitar da N115.4 billion don fadada titin Kano-Kazaure-Kongwalam
- Gwamnatin tarayya za ta fara aikin fadada titin da ya hada jihohin Kano, Jigawa da Katsina
- Majalisar zartaswa ta amince da kudi bilyan dari da sha biyar don fadada titin mai tsawon kilomita 130
- Minista Raji Fashola ya ce za'a kwashe shekaru biyu ana aikin kafin a kammala
Abuja - Majalisar zartaswar tarayya (FEC) ta amince da fitar da N115.4 billion don fadada titin Kano-Kazaure-Kongwalam dake hada jihohiin Kano, Jigawa da Katsina.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana hakan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa bayan taron FEC, rahoton PT.
Yace:
"Ma'aikatar Ayyuka da gidaje ta gabatar da bukatar fadada titin Kano-Kazaura-Kongwalam, mai tsayin kilomita 131.4, daga mai baki daya zuwa baki biyu."
"Saboda haka majalisar zartaswa ta amince da kudi N115, 425, 896,907.15 na tsawon watanni 48.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamfanin BUA zai gina titin
A cewarsa, an kyautata zaton za'a kammala aikin cikin shekaru biyu karkashin tsarin 'Tax credit Scheme.'
Tsarin 'Tax credit Scheme' wani tsari ne da gwamnati ta fitar inda manyan attajirai masu kamfanoni a Najeriya zasuyi amfani da kudin haraji wajen wasu manyan ayyuka maimakon biyan kudin harajin asusun gwamnati.
Fashola yace kamfanin BUA zai bada kudin ginin wannan titi kuma kamfanin PW za'a baiwa kwangilan.
Yace:
"Kamfanin BUA zai bada kudin ginin karkashin tsarin 'Tax Credit Scheme'. Kuma kamfanin PW za'a baiwa kwangilan."
Gwamnatin tarayya na gina tituna 21 a jihar Kano, Minista Fashola
A wani labarin kuwa, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya na aiki kan titunan da jimmilan tsayinsu ya kai kilomita 960 guda 21 a jihar Kano.
Ministan ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kaiwa Gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje a Kano.
Diraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar aiki, Boade Akinola ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Yace a yanzu Gwamnatin tarayya na ayyukan tituna 21 a matsayin a Kano da kewaye kuma jimillan tsayinsu ya kai kilomita 960.
Daga cikin wadanda suka shahara sune Titin Kano-Abuja, Kano-Katsina, Kano-Maiduguri, dss.
Asali: Legit.ng