'Diyar Atiku ta baiwa dan wasan Nollywood kyautar fulotin fili a Abuja

'Diyar Atiku ta baiwa dan wasan Nollywood kyautar fulotin fili a Abuja

  • Daya daga cikin 'yayan babban jigon jam'iyyar PDP ta baiwa dan wasan kwaikwayo kyautan fili a Abuja
  • Nana Atiku ta siffanta Zubby Micheal, matsayin dan wasan da tafi son yadda yake wasansa
  • Zubby Micheal ya bayyana farin cikinsa da wannan kyauta kuma ya mika godiya da addu'a

Diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Nana Atiku, ta baiwa wani jarumin wasan kwaikwayon Nollywood, Zubby Micheal, kyautar fulotin fili don murnar ranar haihuwarsa.

A shafinsa na Instagram, Zubby ya daura hotonsa na Nana Atiku inda ya bayyana ta bashi kyautar fili.

Jarumin ya yi mata addu'a kuma ya yi godiya.

Yace:

"Babban kyautan ranar haihuwa mafi kyau. NANA ATIKU ta bani kyautar fulotin fili a Abuja matsayin kyaut. Nagode sosai, Allah yayi albarka."

Kara karanta wannan

Na kusa na yi wuff da ke idan Allah ya yarda – Lilin Baba ga Ummi Rahab

'Diyar Atiku ta baiwa dan wasan Nollywood kyautar fulotin fili a Abuja
'Diyar Atiku ta baiwa dan wasan Nollywood kyautar fulotin fili a Abuja Hoto: @Nanaatiku_kadi
Asali: Instagram

Hakazalika Nana Atiku ta daura hotunanta da Zubby a shafinsa na IG inda ta tayashi murna.

Tace:

"Ina taya dan fim din da nafi so murnar ranar haihuwa. Ina alfahari da kai."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: