Abu ya girmama: Yan kungiyar asiri sun kashe mataimakin kwamishinan yan sanda
- Wasu miyagun yan ƙungiyar asiri sun hallaka mataimakin kwamishinan yan sanda mai ritaya a jihar Imo
- Bayanan da muka samu sun nuna cewa mambobin ƙungiyar asirin sun farmaki ACP ɗin ne a gidansa ranar Laraba, suka masa kisan gilla
- Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo ya tabbatar da cewa ya ji labarin amma bai samu bayani a hukumance daga DPO na yankin ba
Imo - Mazauna yankin Agwa clan dake karamar hukumar Oguta, jihar Imo sun shiga jimami biyo bayan kisan gillan da akai wa mataimakin kwamishinan yan sanda mai ritaya kuma lauya, Barista Christian Kpatuma.
The Nation ta tattaro cewa marigayi mataimakin kwamishina (ACP) wanda aka fi sani da "Hippies" ana zargin ya rasa ransa ne a hannun wasu yan kungiyar asiri.
Rahotanni sun nuna cewa yan kungiyar asirin waɗan da sanannu ne a yankin Agwa, sun je har cikin gidansa da safiyar Laraba, kuma suka kashe shi.
Wani sanannen mutumi a yankin da abun ya faru, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya roki gwamna Hope Uzodinma, na jihar Imo ya yi duk me yuwu wa wajen hukunta waɗan da suka kashe marigayi ACP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Punch ta ruwaito Mutumin yace:
"Ina kira ga mai girma gwamna ya jibge jami'an tsaro a Agwa da nufin su farauto waɗan nan yan ƙungiyar asirin da mutanen da suka ɗauki nauyin su, har sai an hukunta su."
"Mutanen Agwa na rayuwa cikin fargaba, duk da 'ya'yan yankin ne suka kafa Hedkwatar yan sanda (wacce ake alfahari da ita a jihar Imo), kwana uku kacal da ƙaddamar da ita, tare da Yan Bijilanti. Gaskiya ina cikin takaici."
Shin hukumar yan sanda ta samu rahoto?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, CSP Michael Abattam, yace ya ji labarin faruwar lamarin, amma har yanzun bai samu bayani a hukumance daga DPO na yankin ba.
"Na ji labarin abin da ya auku, amma ina son samun bayanai a hukumance daga DPO na yamkin, kafin na dawo gare ku."
A wani labarin na daban kuma Ɗan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan gyaran hali saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar
Kotu ta ɗage sauraron karar tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Muazu Magaji saboda ta yi karo da shari'ar Sheikh Abduljabbar.
A halin yanzun an ɗage ta Ɗan sarauniya zuwa 4 ga watan Fabrairu, 2022, yayin ta Malam Abduljabbar zata wakana 3 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng