Gwamnan bankin CBN ya bude katafaren kamfanin shinkafa da zai taimakawa Jihohin Arewa

Gwamnan bankin CBN ya bude katafaren kamfanin shinkafa da zai taimakawa Jihohin Arewa

  • Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bude kamfanin casar shinkafar Gerawa Rice Mill a jihar Kano
  • Godwin Emefiele ya ce wannan yana cikin kokarin gwamnatin Buhari na bunkasa harkar noma
  • Wannan kamfanin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, sannan shinkafa za ta kara yalwata

Kano - A ranar Talata, 1 ga watan Fubrairu 2022, Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefiele ya bude wani kamfanin shinkafa a jihar Kano.

Gidan talabijin na TVC ya kawo rahoto a ranar Larabar nan cewa wannan kamfani na zamani zai iya cashe abin da ya kai metric tona 420 na shinkafa kowace rana.

Da yake jawabi a bikin kaddamarwar, Godwin Emefiele ya ce wannan kamfani zai taimaka wajen samar da isasshen abinci kamar yadda gwamnatin nan ta ke da buri.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Solacebase ta ce Mista Godwin Emefiele ya yi kira ga masu kamfanonin casar shinkafa su hada-kai da kungiyar manoma wajen samar da shinkafan da za a rika ci.

Shawarar Godwin Emefiele

“Yayin da mu ke kara adadin shinkafar da za mu iya cashewa a fadin kasar nan, mu na kira ga masu casar shinkafa su rungumi tsarin da muka kawo.”
“Su shiga harkar samar da shinkafar da za a ci domin a samu isassun shinkafar da za a rika aiki kansu daga wajen kananan manoma.” – Gwamnan CBN.
Gerawa Rice Mills
Kamfanin Gerawa Rice Mills Hoto: Onovwo Omasoro Ali Ovie / Twitter
Asali: Twitter

A karkashin tsarin da CBN suka kawo, za a ba masu casar shinkafa damar bude gonaki, kafa wajen noman rani da duk abubuwan da ake bukata domin a samu abinci.

Emefiele yake cewa shinkafar da za a rika samu a Najeriya za ta yi takara da wadanda ake ci a kasashen waje. Isa Gerawa ya ce yanzu an fi sha'awar cin shinkafar gida.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Kafin a fara shirin ‘Anchor Borrowers’ a Najeriya, kamfanonin casar shinkafar da ake da su ba su wuce 10 ba, yanzu ana da 60 baya ga wasu 10 da za a bude a shekarar bana.

Da yake jawabi, gwamna Abdullahi Ganduje ya ce Kano tana amfana da ruwa da suka zagaye ta don haka manoma suke noma shinkafa, tumatur da sauran kayan gona.

Gwamnonin Kebbi da Jigawa, Badaru Abubakar da Atiku Bagudu sun halarci bikin bude wannan kamfanin N15bn da Alhaji Isa Gerawa ya kafa mai suna Gerawa Rice Mill.

Rashin tsaro a Kaduna

A jihar Kaduna kuwa an ji cewa alkaluman da aka fitar a makon nan sun nuna a duk ranar Duniya sai miyagun ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 9 a shekarar 2021.

Gwamna Nasir El-Rufai ya ba Gwamnatin Tarayya shawarar yadda za a kawo karshen kashe-kashe da satar mutane da ake fama da shi a yankin Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng