An tura matashi zaman gidan yarin shekara kan laifin zambar N15.4m a Maiduguri

An tura matashi zaman gidan yarin shekara kan laifin zambar N15.4m a Maiduguri

  • An baiwa matashi kudi ya sayi baburan Keke Napep amma yayi awon gaba da kudin don amfanin kansa
  • Hukumar EFCC ta cika hannu da shi kuma an gurfanar da shi gaban kotu a birnin Maiduguri
  • An yanke masa hukuncin shekara guda a gidan yari kuma ya mayar da kudin da aka bashi milyan 15

Borno - Babbar kotun jihar Borno ta jefa wani matashi masi suna Bashir Mohammed Karube gidan gyara hali na tsawon shekara guda bisa laifin damfara da zamba.

Wannan ya biyo bayan gurfanar da shi da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tayi kan laifin damfara kudin sama da milyan sha biyar.

Hukumar ta bayyana cewa matashin ya karbi kudi hannun wan don ya saya masa keken A daidaita sahu amma yayi awon gaba da kudi.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

EFCC a jawabin da ta sake ranar Litinin tace:

"A ranar litinin, 31 ga watan Janairu, 2022, mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Barno ta yanke ma wani mai suna Bashir Mohammed Karube hukuncin zaman gidan yari na shekara daya bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi inda take tuhumar shi da laifin cin amana ta kudi kimanin Naira miliyan goma sha biyar da dubu dari hudu.
Hukumar EFCC ta tuhume shi da karban kudin a hannun wani mai suna Mohammed Bukar Customs da niyyar siyo masa Keke Napep guda ashirin amma daga baya ya karkatar da kudin.
Wanda aka tuhuma ya musanta laifin dalilin da ya sa aka fara sauraren shari’a da gabatar da shaidu biyar da sauran hujjoji."

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Maiduguri
An tura matashi zaman gidan yarin shekara kan laifin zambar N15.4m a Maiduguri Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Hukuncin kotu da sharadin da aka sanya masa

Mai shari'a Aisha Kumaliya ta bukaci matashi ya mayar da kudin da ya karkatar ko kuma a jefa shi gidan yarin shekaru goma.

Jawabin ya kara da cewa:

"A lokacin yanke hukuncin, mai shari’a Kumaliya ta kama Karube da laifin sannan ta yanke masa hukuncin zama gidan yari na shekara daya ko biyan tara da Naira dubu hamsin.
Sannan mai shari’a ta umarcee shi da ya mayarwa wanda ya zambata kudinshi Naira miliyan goma sha biyar ko kuma ya yi zaman shekaaru goma a gidan yari."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng