Da duminsa: Atiku ya kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB

Da duminsa: Atiku ya kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB

  • Atiku Abubakar ya shiga jerin yan siyasan da suka kai ziyarar jaje da jihohin dake fama da matsalar tsaro
  • Hakazalika ya shiga jerin masu neman kujeran shugaban kasan da suka kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB
  • Har yanzu Atiku bai bayyana niyyar takara a zaben 2023 ba amma ana hasashen zai yi

Neja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigon jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara wajen tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida.

Atiku ya dira Minna, birnin jihar Neja ne ranar Talata, 1 ga watan Febrairu, 2022, rahoton Vanguard.

Sun yi ganawar sirri na tsawon kimanin sa'a guda kuma bai bayyana dalilin ziyararsa ba.

Amma an tattaro cewa ziyarar bata da alaka da neman kujeran shugaban kasa da Atiku ke yi.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan takararsa ta shugaban ƙasa a zaben dake tafe 2023

Da duminsa: Atiku ya kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB
Da duminsa: Atiku ya kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB
Asali: Facebook

A hirar da yayi da manema labarai bayan tattaunawar, Atiku yace ya kai ziyarar gidan gwamnatin jihar ne don jajantawa gwamnan bisa kashe-kashen mutane da ke faruwa a jihar.

Atiku yace:

"Kawai na kawo wa gwamnan ziyarar jaje ne bisa matsalar tsaro a jihar Neja. Na tattauna da Gwamnan kan lamarin rashin tsaro."
"Abin takaici ne kuma babu dadi."

Atiku Abubakar ya bayyana lokacin da zai ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sanar da shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa lokacin da ya dace.

TVC News ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban ya faɗi haka ne bayan ganawa da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a fadar gwamnatin jihar dake Minna, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan fito wa daga ganawar sirri da gwamna Abubakar Bello, Atiku yace yana jiran lokacin da ya dace kuma nan bada jimawa zai bayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng