Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa ta ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a Arewa

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa ta ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a Arewa

  • Majalisar dattawa ta amince da manyan muhimman kudirori da suka shafi makarantun gaba da sakandire a Najeriya
  • A zamanta na yau Talata, Sanatocin sun amince da ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a jihar Kwara
  • Kazalika sun amince da kudirin jami'o'in fasaha na tarayyan Najeriya 2004 wanda suka yi wa kwaskwarima

Kwara - A ranar Talata, majalisar dattawan Najeriya ta amince da kafa makarantar koyar da ilimin ma'adanan ƙasa da ilimin halitta a Guyuk.

Haka nan kuma majalisar ta amince da ɗaga darajar kwalejin fasaha (Poly) Offa, jihar Kwara, daga mai bada Diploma zuwa Jami'a mai bada takardar shaidar kammala Digiri.

Sannan kuma majalisar ta sake amincewa da kudirin jami'o'in fasaha na tarayyan Najeriya 2004 wanda ta yi wa garambawul.

Kwalejin Fasaha dake Kwara
Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa ta ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a Arewa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Majalisar dattawan ta amince da waɗan nan kudirori ne biyo bayan nazarin da ta yi kan rahoto biyu da kwamitin TETFUND da kuma kwamitin makarantun gaba da Sakandire suka gabatar mata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa zai fara neman shawara kan ko ya cancanta ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kwamitin, Sanata Ahmad Babba Kaita, yace kafa makarantar koyar da ilimin ma'adanai da ilimin halittun ƙasa zai taimaka wajen samar da horo da kwarewar kayan aiki ga sashin ma'adanai.

Ya ƙara da cewa makarantar zata haɗa hannu da wasu manyan makarantu na duniya wajen cigaban waɗannan ilimin da kuma ƙarfafa wa malaman makaranta guiwa wajen aikin su da ba su horo.

Sanatan yace:

"Makarantar da za'a kafa ta koyar da ilimin albarkatun ƙasa da ilimin halitta zata taimaka wajen samar da kayan aiki ga ɓangaren kula da ma'adanan ƙasa a Najeriya."

Ɓarayi sum afka Hostel ɗin mata a BUK

A wani labarin na daban kuma Ɓarayi sun fasa Hostel ɗin mata a jami'ar BUK, sun aikata mummunar ta'asa

Wasu Barayi sun kutsa cikin dakin kwanan ɗalibai mata a jami'ar Bayero University Kano , sun sace manyan wayoyi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta tura tsohon kwamishina Ɗan Sarauniya gidan gyaran hali

Ɗaliban da lamarin ya shafa sun shiga matuƙar damuwa, domin har da sabbin wayoyin IPone daga cikin waɗan da aka sace.

An tattaro cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Litinin a gidan kwanan mata Ramat Annex female hostel dake sabon ginin BUK.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262