Rudani: Matar Atiku ta koka kan yadda yaransa ke barazanar kasheta don ta nemi saki

Rudani: Matar Atiku ta koka kan yadda yaransa ke barazanar kasheta don ta nemi saki

  • Daya daga cikin matan Atiku Abubakar, Jennifer Douglas Abubakar, ta yi kukan barazanar kisa da ake yi mata
  • Jennifer a wata hira a baya-bayan nan ta ce barazanar ta fara ne bayan ta bayyana shirinta na rabuwa da Atiku Abubakar
  • Matar tsohon mataimakin shugaban kasar ta uku ta musanta zargin cewa tana shirin barin auren ne saboda ya auri wata mata

Matar Atiku Abubakar ta uku, Jennifer Douglas Abubakar, ta yi ikirarin cewa tana fuskantar barazanar kisa sakamakon shirinta na rabuwa da tsohon mataimakin shugaban kasar.

Jennifer, wacce lauya ce a kasar Amurka ta musanta zargin cewa tana yunkurin rabuwa da Atiku saboda kwanan nan ya auri sabuwar amarya ba tare da sanar da ita ba kamar yadda al’adar Arewa da Musulunci suka tanada, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

Barazana a gidan Atiku
Rudani: Matar Atiku ta koka kan yadda yaransa ke barazanar kasheta don ta nemi saki | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A maimakon haka, ta bayyana cewa aniyar ta na neman sakin yana da nasaba ne da shawarar zama a Amurka don kula da ‘ya’yanta wadanda a cewarta, sun dade ba tare da iyayensu ba, in ji PM News.

Ta kara da cewa akwai batutuwan da suka dade a gamayyar auren nasu wanda kuma shi ne dalilin da ya sa ta yanke wannan shawarar.

Da take karin haske, matar dan takarar shugaban kasan ta ce a yanzu haka tana samun barazanar kisa daga jami’an tsaronsa tun bayan da ta bayyana shirin ta na rabuwa da shi.

A kalamanta:

“Cewa Mai Martaba ya auri amarya ba shi ne ya kawo matsala tsakaninmu ba kamar yadda mutane da yawa ke cewa. Mai Martaba Musulmi ne, ban taba tambayarsa game da matansa ko nufinsa ba.

Kara karanta wannan

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

“Babban dalilin neman kashe aurena shi ne rashin jituwa game da ci gaba da zama a Burtaniya, don kula da ’ya’yana da wasu batutuwa da suka dade a kasa.
"Tun da wannan lamarin, ina jin tsoratarwa kaina da na 'ya'yana. Jami’an tsaronsa na musamman Ibro da sauran su suna ta barazana da kiraye-kirayen ‘yan uwa da abokai da ma’aikata suna neman kadarorina su kwace.
“Saboda haka, na fice daga tawagar lauyoyi na, na sayar da dukiyoyina kuma na koma kasar waje har zuwa lokacin da zaman lafiya ya samu.
"Ban yi wani laifi ba face na nemi a raba aurena kuma abin ya min zafi da har nayi amfani da wannan kafar wajen magance matsaloli masu sarkakiya amma ina fargabar cewa a wannan lokaci zan sanya bangarena a rubuce."

Da addu'a zamu karbi mulkin Najeriya, matar Atiku ta magantu kan shirinsu a zaben 2023

A bangare guda, Misis Titi Abubakar, uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ta bayyana cewa za ta kara masa kwarin gwiwar sake tsayawa takarar shugaban kasa a karo na biyu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Atiku haifaffen jihar Adamawa yana yunkurin zama shugaban Najeriya tun a shekarun 1990.

Akwai jita-jita cewa shahararren dan siyasan zai sake lalubar damar tsayawa takara a zaben 2023.

Uwargidansa Titi, ‘yar asalin jihar Osun, ta ce da ikon Allah, mijinta zai zama shugaban kasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.