Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da asusun lamunin kawar da cutar Kanjamau N62bn

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da asusun lamunin kawar da cutar Kanjamau N62bn

  • Bayan shekara da shekaru ana yakar Kanjamau a Najeriya, har yanzu da sauran rina a kaba
  • Shugaban kasa ya kaddamar da asusun lamunin N62bn don takaita yaduwar cutar a fadin Najeriya
  • Manyan attajiran Najeriya ne zasu bada gudunmuwan kudade wajen gudanar da ayyukan asusun

Abuja - A ranar Talata, 1 ga Febrairu, Shugaba Muhammadu Buhari da manyan jami'an gwamnati da attajirai sun dira taron kaddamar da asusun lamunin cutar Kanjamau HIV/AIDS.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnati ba za tayi kasa a gwiwa wajen takaita yaduwar cutar ba.

Shugaban kasan ya jinjinawa hukumar takaita yaduwar cutar HIV, NACA.

Legit ta halarci taron da ya gudana a fadar Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

"Daga yanzu, ina kyautata zaton asusun lamunin HIV zai taimaka wajen cimma manufar kawar da yaduwar Kanjamau nan da shekaru biyar."

An addamar asusun lamunin kawar da cutar Kanjamau N62bn
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar asusun lamunin kawar da cutar Kanjamau N62bn
Asali: Original

Hukumar NACA ta kafa asusun lamunin ne domin yaki da yawaitar masu kamuwa da cutar HIV a Najeriya.

Mambobin kwamitin dattawan asusun sun hada da shugaban bankin Access, Herbert Wigwe; Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote; Dirakta Manajan Total, Mike Sangster; da Managan kamfanin man Shell, Osaguue Okunbor.

Sauran sune shugaban kamfanin Julius Berger, Lar Richter; Shugaban hukumar NACA, Gambo Aliyu; da tsohon shugaban hukumar NACA, Aliyu.

An nada Jekwu Ozoemene matsayin shugaban kwamitin asusun lamunin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng