Babbar Magana: Ɓarayi sun fasa Hostel ɗin mata a jami'ar BUK, sun aikata mummunar ta'asa
- Wasu Barayi sun kutsa cikin dakin kwanan ɗalibai mata a jami'ar Bayero University Kano, sun sace manyan wayoyi
- Ɗaliban da lamarin ya shafa sun shiga matuƙar damuwa, domin har da sabbin wayoyin IPone daga cikin waɗan da aka sace
- Sai dai mahukuntan jami'ar na ganin waɗan da suka aikata satar na cikin matan dake Hostel ɗin, amma ɗaliban sun ce ba haka ba ne
Kano - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa aƙalla wayoyin hannu 17 aka tabbatar ɓarayi sun sace yayin da suka kutsa cikin gidan ɗalibai mata a jami'ar BUK dake Kano.
An tattaro cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Litinin a gidan kwanan mata Ramat Annex female hostel dake sabon ginin BUK.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ɗaliban dake Hostel ɗin sun shiga tashin hankali saboda faruwar lamarin.
Wata daga cikin ɗaliban da satar ta shafa, tace sun gane an sace musu wayoyi ne lokacin da wasu suka tashi da misalin ƙarfe 3:00 na dare domin yin karatu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ƙara da cewa ginin Hostel ɗin, wanda asalinsa Asibitin makaranta ne, ya lalace sabida watsin da aka yi da shi, kuma gilasai duk sun farfashe.
Ɗalibar, wacce ta nemi a sakaya sunanta tace sun kulle kofofin dakunan su kafin su kwanta bacci, amma da suka farka sai suka ga kofofi a buɗe.
Ya ɗaliban suka yi bayan gano abin da ya faru?
Bugu da ƙari ɗalibar ta ce bayan gano an musu sata, ba su yi wata-wata suka sanar da jami'an tsaron jami'ar dake Hostel ɗin, amma sai suka faɗa musu idan safiya ta yi su je ofishin tsaro su kai kukansu.
Wata ɗalibar kuma da lamarin ya shafa, ita ma ta nemi kada a faɗi sunanta, ta ce sun yi matuƙar mamaki da suka gano ba abin da jami'an tsaron makaranta ke yi na kamo ɓarayin.
A cewarta, maimakon haka sai suka koma suna zargin su da cewa masu ɗan hannun suna cikin mu, duk da kwararan hujjojin da suka gabatar musu na cewa ba haka bane.
Tace:
"Wasu wayoyin suna da tsada domin akwai IPone na baya-bayan nan da sauran manyan wayoyi. Amma mu ba wannan ne ya fi damun mu ba."
"Abin da muke tsoro shi ne idan har ɓarawo ko ince ɓarayi za su aikata wannan ta'asa cikin nasara, wa zai ce ma su cin zarafin mata ba za su samu nasara ba? Wannan ne ya sa muka damu matuƙa."
Rahotanni sun bayyana cewa lokacin da matan suka jaraba kiran lambobin wayar da aka sace, wani Namiji ne ya ɗauka amma daga baya ya katse kiran.
Wane mataki aka ɗauka zuwa yanzun?
Yayin da muka tuntubi kakakin jami'ar, Lamara Garba, yace zai bincika ya tabbatar kafin ya dawo gare mu.
Sai dai wata majiya daga jami'ar, ta bayyana cewa jami'an tsaron BUK sun ce akalla wayoyi 12 aka sace, amma suna ganin waɗan da suka aikata na cikin ɗaliban, domin babu wasu hujjoji da suka tabbatar da shiga aka yi.
A wani labarin kuma Babban ɗan marigayi Sheikh Albany Zariya ya bayyana wata muhimmiyar wasiyya da Malam ya bar musu
Yayin da Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albany Zaria ke cika sheƙara 7 da rasuwa, an yi fira da babban ɗansa, Abdulrahman.
Abdulrahman Muhammad Auwal, ya bayyana wata wasiyya da Mahaifinsa ya bar musu, wacce ba za su manta da kalaman malamin ba.
Asali: Legit.ng