1st Class: Bahaushiya a jami'ar ABU ta kafa tarihin da ba a taba ba a fannin Mathematics

1st Class: Bahaushiya a jami'ar ABU ta kafa tarihin da ba a taba ba a fannin Mathematics

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta birge mutane da dama da kwazon da ta yi a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna
  • Zainab Bello ta karya tarihin shekaru 60 a sashen ilimin lissafi na jami'ar, inda ta zama daliba ta farko da ta kammala da 1st class
  • Baiwar Allahn ance ta kasance tauraruwa tun daga lokacin da take makarantar renon yara, inda take samun sakamako mai kyau tun tana karama

Zaria, Kaduna - Tun lokacin da aka kafa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1962, babu wata daliba mace da ta gama digiri da 1st class a fannin lissafi. To, wannan tarihin mai shekaru 60 ya rushe da wata baiwar Allah wacce aka fi sani da Zainab Bello.

Zainab ta gama da CGPA mai ban sha'awa na 4.85, tarihin da ba a taba samu ba. An kafa Sashen Lissafi na ABU ne a shekarar 1962, a shekarar ne aka kafa jami'ar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta yi kaca-kaca da wani gidan mai mallakar ministan Buhari

Matashiya mai 1st class
1st Class: Matashiya bahaushiya a jami'ar ABU ta kafa tarihin da ba a taba ba a fannin Mathematics | Hoto: Mohammed Ali
Asali: Facebook

Ta kasance mai kwazo tun tana makarantar renon yara

Fara samun nasara irin wannan ba bakon abu bane a wurin Zainab. Wani rubutu da Mohammed Ali ya yi a Facebook ya nuna cewa a dama ta kasance mai kwazo tun lokacin karatunta na nasire.

A cewar rubutun na Ali:

"Wannan Zainab Bello kenan zakakurar dalibar da ta kammala karatun digiri na farko da 1st class (CGPA 4.85 a tsangayar lissafi ta ABU Zaria kuma mace ta 1 da ta kammala da irin wannan sakamako.
"Tana da matukar kokari tun daga nasire, kuma kunsan wani abu? Hafiza ce ta haddace Alqur'ani mai girma tana da shekaru 11), ina taya ki murna da fatan Allah ya albarkace ki da satifiket dinki."

Martanin murna daga 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Mata 3 da suka yi wa maza zarra, suka fita da digirin ‘First Class’ a ABU Zaria a 2020/21

‘Yan Najeriya da dama da suka ga yadda Zainab ta yi kokari sun taya ta murna a kafafen sada zumunta.

Ga kadan daga fatan alherin 'yan Najeriya

Felix Okwudili Anibis ya ce:

"Ina taya ki murna da karin kaimi ga kokarinki."

Garba Isa ya rubuta:

"Ina miki fatan alheri a cikin aikinki na gaba."

Na'Annabi Sagir Muazu yayi sharhi da cewa:

"Ina taya yarinyar nan murna, ta cancanci yabo, karfafawa, kwarin gwiwa da addu'a."

Yunusa Ibrahim Tafida Mk yace:

"Ina tayaki murna da fatan Allah ya kara miki albarka ranki ya dade kuma first class a fannin lissafi."

A baya kunji cewa, a ‘yan shekarun nan, mata sun dage a harkar boko kuma su na yin zarra. A wannan rahoto mun tattaro wasu daidaikun matan da suka zama zakaru.

A jerin za a ji labarin Musa Muminah Agaka, Zainab Bello da kuma Malam Asmau Jibril.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.