‘Yan Sanda sun cafke miyagu sama da 50 da ke tare da gawurtaccen ‘Dan bindiga Turji

‘Yan Sanda sun cafke miyagu sama da 50 da ke tare da gawurtaccen ‘Dan bindiga Turji

  • Rahotanni daga Aminiya sun bayyana cewa ‘yan sanda sun kama miyagun mutane 57 a Sokoto
  • Ana zargin cewa miyagun ‘yan bindigan da suka shiga hannu, su na tare ne da Muhammad Bello Turji
  • Jami’in ‘yan sandan Najeriya ya bayyana wannan da yake yi wa ‘yan jarida jawabi a garin Sokoto

Aminiya ta fitar da rahoto a yau Litinin, 31 ga watan Junairu 2022, ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kai wani farmaki, sun yi ram da yaran Bello Turji.

Dakarun ‘yan sandan na Najeriya sun yi dace sun damke wadannan ‘yan bindiga ne da suka kai farmaki a garuruwan Goronyo, Rabah da Illela duk a Sokoto.

Mataimakin sufeta na ‘yan sanda, DIG Zaki M. Ahmad ya jagoranci farmakin da aka kai, har aka kama mutane 37 da ake zargin cewa miyagun ‘yan bindiga ne.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

An kuma cafko gama-garin mutane 20 da ake tuhuma da laifin alaka da wadannan ‘yan bindiga.

An dace - Zaki M. Ahmad

Jaridar Aminiya ta ce Zaki M. Ahmad ya kira taron manema labarai a garin Sokoto, inda ya yi wa ‘yan jarida bayanin irin nasarorin da jami’an tsaro suka samu.

M. Ahmed ya ce rundunar ‘yan sanda ta kama wadannan mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne a yankunan Gudugudu, Illela, Heli, Goronyo, Mayel, da Sakanau.

‘Yan Sanda
Kayan fadan 'Yan bindiga Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

Jami’an tsaron sun kuma cafke sauran mutanen nan a Kuka, Zangon Isu, Tsamaye, Dunawa, Tangaza, Isa, da kauyukan Bungo, Sangari duk a jihar Sokoto.

Baya ga cafke ‘yan bindigan, jami’in ya ce sun karbe wasu makamansu. Mataimakin sufetan ‘yan sandan ya ce miyagun makamai aka rika samu a hannunsu.

“Dukkannin wadanda aka kama suna da alaka da ayarin sanannen dan bindigar nan Bello Turji, kuma sun fadi cewa suna aikata miyagun laifukffuka na fashin daji.

Kara karanta wannan

2023: Malaman addinin Musulunci da Kirista fiye 1,000 sun yi taron yi wa gwamnan APC addu’o’in samun nasara

“Haka kuma ana cigaba da bincike kan lamarin, da zaran an kammala za a kai wadanda ake zargi gaban shari’a, domin Alkali ya hukunta su” - Inji DIG Zaki M. Ahmad.

Sai kuma me aka samu?

An samu shanu 150 da bindigogin AK-47 har 32 da harsasai 2,700. Sannan kuma akwai babbar bindiga mai harbo jirgi, da babur, wayoyin salula 16 da kuma allurer Penta.

Musa Kamarawa su na hannu

Yaran ‘dan ta’addan da suka shiga hannu sun hada da likitan ‘yan bindigan, Abubakar Hashimu Kamarawa da mai taimaka masu da makamai, Musa Kamarawa.

Kwanakin baya ne aka ji cewa Musa Kamarawa wanda na-kusa ne da Muhammad Bello wanda aka fi sani da Turji ya fasa-kwan ta'adin da shi da mutanensu ke yi.

Wannan Bawan Allah ya fadi sirrin Turji da abokan aikinsu da masu taimaka masu da kayan yaki da sauran abubuwan da suke bukata, ya ce yana na nadama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng