Da Dumi-Dumi: Kotu ta tura tsohon kwamishina Ɗan Sarauniya, gidan gyaran hali

Da Dumi-Dumi: Kotu ta tura tsohon kwamishina Ɗan Sarauniya, gidan gyaran hali

  • Kotun dake sauraron shari'ar tsohon kwamishina, Muazu Magaji, ta aike da shi gidan Yari har zuwa lokacin da zata sake zama
  • Alƙalin kotun, Mai Shari'a Aminu Gabari, ya umarci a cigaba da tsare Ɗan Sarauniya, kuma a tura likitoci su duba lafiyarsa
  • Tsohon kwamishinan ya musanta tuhume-tuhumen da ake masa, da suka haɗa da zagin gwamna Ganduje

Kano - Kotun Majistire dake zamanta a Nomansland, ta ba da umarnin cigaba da tsare tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, a gidan gyaran hali.

BBC Hausa ta rahoto cewa an gurfanar da tsohon kwamishinan, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya, a gaban kotun bisa zargin bata sunan gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano.

Muazu Magaji Ɗan.Sarauniya
Da Dumi-Dumi: Kotu ta tura tsohon kwamishina Ɗan Sarauniya, gidan gyaran hali Hoto: BBC Hausa/facebook
Asali: Facebook

Alƙalin Kotun, Mai shari'a Aminu Gabari, shi ne ya baiwa jami'an tsaro umarnin cigaba da tsare Ɗan Sarauniya a zaman sauraron ƙarar da ya gudana yau Litinin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana shirin da yake na gaje kujerar Buhari a 2023

Haka nan kuma, Alkalin ya ba da umarnin a tura Likitoci na musamman su duba lafiyar wanda ake zargi, wanda ya yi ƙaurin suna wajen cacakar Ganduje, a Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan haka, sai mai shari'a Gabari ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa wata mai kamawa, ranar 2 ga watan Fabrairu, 2022.

Kazalika ya umarci Lauyoyin bangarorin guda biyu, wanda ake kara da masu shigar da ƙara, su haɗa kundin shari'ar kuma su kai masa a ranar zama na gaba.

Shin Ɗan Sarauniya ya amsa tuhumar da ake masa?

Tsohon kwamishinan, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ko Win-Win, ya musanta dukkan zargin da ake masa a zaman kotun na yau.

Bayan zayyano masa dukkan tuhumar da ake masa, Ɗan Sarauniya ya musanta aikata ko ɗaya daga cikin su nan take, kamar yadda Premium Times ta ruwaito

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Masu zanga-zanga daga tsagin Ganduje da Ɗan Sarauniya sun mamaye kotun da ake Shari'ar a Kano

Zagin gwamna Ganduje na jihar Kano, karya, tunzura al'ummar jiha da kuma ɓata sunan Ganduje, su ne tuhume-tuhumen da ake masa amma yace sam bai aikata ko ɗaya ba.

A wani labarin na daban kuma Wani mutumi ya Musulunta saboda kallon shirin IZZAR SO na masana'antar Kannywood

Wani bawan Allah ya karbi kalmar shahada ya shiga Addinin Musulunci saboda kallon shirin Izzar So da yake yi.

Lawan Ahmad wato Umar Hashim a shirin Izzar So, shine ce ya faɗi haka, kuma ya sanya bidiyon mutumin na maimata kalmar shahada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262