Jami'ar Nijar: Jami'a ta sanya wa titi sunan marigayiya Hanifa Abubakar
- Jami'ar Maryam Abacha da ke jamhuriyar ta sanya wa wani titi a cikin jami'ar sunan marigayiya Hanifa
- Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan gano wani makashi ya hallaka Hanifa bayan sace ta da kwanaki
- A wasu hotunan da muka samo, an ga wasu jami'an jami'a na kaddamar da titinn, inda aka rubuta 'HANEEFA ABUBAKAR ABDULSALAM STREET"
Jamhuriyar Nijar - Wata jami'a a jamhuriyar Nijar, Maryam Abacha American University ta sanyawa wani titi sunan Hanifa Abubakar Abdulsalam.
Hanifa Abubakar, wata yarinya mai shekaru 5, an yi mata kisan gilla a jihar Kano, bayan da wani malami kuma shugaban makaranta ya sace ta.

Source: Facebook
Bayan kisan Hanifa, jama'a da dama sun damu matuka kan labarin, lamarin da ya kai ga tsoma baki daga gwamnatin Kano da ma na Najeriya.
A wasu hotunan da Legit.ng Hausa ta samo a shafin Arewa , an ga wasu jami'an jami'ar na jikin allon da titin da aka sanyawa suna 'HANEEFA ABUBAKAR ABDULSALAM'
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli hotunan a kasa:

Source: Facebook

Source: Facebook
An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai
A wani labarin, Jamila Muhammad Sani, matar makashin Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5, ta gurfana a gaban babban kotun majistare na jihar Kano da ke zama a Gidan Murtala, Kano, bisa zargin hannu a boye Hanifa.
Jamila, ‘yar shekara 30, matar Abdulmalik Tanko ce, wanda ake shari’a kan tuhume-tuhume hudu da suka hada boye wacce aka yi garkuwa da ita, hada baki, garkuwa da dan mutum da kuma kisan kai.
Mai gabatar da kara, a yayin da take karantawa Jamila rahoton farko na bayanai, ta yi zargin cewa ta boye wacce aka sace a gidanta na tsawon kwanaki biyar.
Asali: Legit.ng
