Kannywood: Bidiyon yadda wani Mutumi da ya karbi Musulunci saboda kallon Fim din Izzar So
- Wani bawan Allah ya karbi kalmar shahada ya shiga Addinin Musulunci saboda kallon shirin Izzar So da yake yi
- Lawan Ahmad wato Umar Hashim a shirin Izzar So, shine ce ya faɗi haka, kuma ya sanya bidiyon mutumin na maimata kalmar shahada
- Mutumin ɗan asalin jihar Cross River ya zaɓi sunan jarumin shirin, Umar, a matsayin sabon sunansa na musulunci
Kano - Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, kuma furodusan shirin 'Izzar So' mai dogon zango, Lawan Ahmad, ya ce wani bawan Allah ya karbi shahada sanadin kallon shirin.
Jarumin ya faɗi wannan kyakkyawan labari ne a wani sakon bidiyo da hotonsa da mutumin, wanda ya sanya a shafinsa na Instagram.
A cikin bidiyon, mutumin ya karɓi kalmar shahada wacce ke shigar da wanda ba musulmi ba zuwa cikin ni'imar musulunci, a kusa da jarumi Lawan Ahmad.
Jarumin yace:
"Masha Allah, a yau ne muka yi babban kamu a musulunci, inda wannan bawan Allah ya shiga musulunci saboda kallon Izzar So da yake yi."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shin mutumin dan ina ne?
Lawan ya ƙara da cewa wanda ya karbi musuluncin ya fito ne daga ƙaramar hukumar Idom Ikon, dake jihar Cross River, kuma ya amince da sunan jarumin shirin, 'Umar' a matsayin sunansa na musulunci.
"Tun daga ƙaramar hukuma Idom Ikon ta jihar Cross River ya taho, yanzu haka ya karbi addinin musulunci. Kuma yanzu haka sunansa ya koma Umar daga John."
Daga karshe Ahmad Lawan, ya yi addu'ar cewa Allah ya sa ya karbi addinin Musulunci a sa'a, kuma Allah ya sa Addinin ya amfane shi da al'umma baki ɗaya.
Shirin Izzar So, wanda har yanzun ake cigaba da yinsa, ya ƙunshi manyan jarumai da suka haɗa da, Ali Nuhu (Matawalle), Lawan Ahmad (Umar Hashim), Aisha Izzar So (Hajiya Nafisa) da sauran su.
A wani labarin na daban kuma Jarumar Kannywood ta koka kan yadda mutane ke kokarin ganin bayan sana'ar da suke yi
Jarumar Kannywood, Sadiya Kabala, ta koka kan yadda mutane ke da taurin bashi idan ka amince ka ba su kayan ka.
Jarumar tace da kasuwanci ne suke samu suna tsira da mutuncin su, musamman idan suka daina harkar shirin fim.
Asali: Legit.ng