Da ɗuminsa: Asari Dokubo ya kira Nnamdi Kanu da IPOB da sakarkaru, ya ce babu yadda za su yi da shi
- Shugaban tsagerun Niger Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya kira IPOB da shugabansu Nnamdi Kanu da sakarkaru
- A cewar Dokubo yayin wani bidiyo da yayi na kai tsaye a Facebook, ya ce sun zarge sa da cin amanar Kanu har aka damko shi daga Kenya
- Duk da ya ce bai san inda shugaban su ya ke rayuwa ba, ya ce shi ne yayi hakan, me za su iya masa?
Shugaban tsagerun yankin Niger Delta, Mujahid Asari Dokubo ya sake suka tare da caccakar 'yan awaren IPOB da shugabansu, Mazi Nnamdi Kanu.
The Nation ta ruwaito cewa, Dokubo ya soki 'yan awaren kuma ya yi musu wankin babban bargo kan cewa da suka yi ya na da hannu wurin dawo da Kanu kasar Najeriya daga Kenya.
The Nation ta ruwaito cewa, Kanu da Dokubo ba su ga maciji kan batun kafa kasar Biafra, dalilin kuma da ya hada su a baya.
Yakin ruwan sanyin ya janyo kafuwar gwamnatin gargajiya ta Biafra wacce Dokubo ya sanar da kafuwar ta a watan Maris din 2020 kuma shi ne shugaban ta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yayin martani a ranar Lahadi yayin wani bidiyon kai tsaye da Dokubo ya yi ta Facebook, ya ce:
"IPOB ta ce ni ne na siyar da su, na ci amanar su bayan ba ni ba ne. Sun ce ni ne na ci amanar shugaban su a Kenya.
“Ban san inda Nnamdi Kanu ya ke rayuwa ba, ban san daga inda ya taho ba. Sun ce ni na siyar da su. Shi ne nace ni ne din, abu na gaba da suka sake cewa shi ne Asari Dokubo ne. Kalla sakarkarun, me za ku iya yi min?"
Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokubo
A wani labari na daban, Mujahid Asari Dokubo, tsohon kwamandan tsageru kuma shugaban gwamnatin gargajiya ta Biafra, ya kwatanta shugaban IPOB da zama dan ta'adda.
A wani bidiyo da ya saki a kafar sada zumunta, Dokubo ya zargi Kanu da amfani da fafutukar Biafra a matsayin wani nau'in kasuwanci.
Ya zargi Kanu da waskar da kudaden da za a yi amfani dasu domin kafa Biafra, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng