Tashin Hankali a Kano: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje ya yi batan dabo

Tashin Hankali a Kano: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje ya yi batan dabo

  • Ɗan kwamishinar mata da harkokin walwala ta jihar Kano, Dakta Zahara'u, ya bata kwanaki 11 kenan da barin gida
  • Rahoto ya bayyana cewa Abdurrahman Abdu Usman, ya bar gida da nufin zuwa Katsina, inda yake bautar ƙasa da aka fi sani da NYSC
  • Dakta Zaharau tace tun wannan lokacin ranar 17 ga watan Janairu, ba'a sake jin ɗuriyarsa ba kuma lambarsa ba ta shiga

Kano - Rahoto daga Kano ya nuna cewa ɗan kwamishiniyar mata da walwalar al'ummar, Dakta Zahara'u Muhammad Umar, ya bata ba'a san inda yake ba.

Rahoton Aminiya ya bayyana cewa iyalan kwamishiniyar na cikin tashin hankali bisa rashin sanin halin da ɗan su, Abdurrahman, ke ciki.

Dakta Zahara'u
Tashin Hankali a Kano: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje ya yi batan dabo Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar 17 ga watan Janairu, 2022, Abdurrahman Abdu Usman, ya bar gida da nufin komawa jihar Katsina wurin da yake aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Kara karanta wannan

Jiga-jigan siyasa, yan kasuwa, attajirai sun dira auren 'dan Dahiru Mangal

Tun bayan tafiyarsa, Abdurrahman, bai tuntuɓi gida ba kuma ko an nemi wayarsa ta hannu ba ta shiga, hakan ya ta da hankulan iyalansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kazalika, Iyalan gidan Dakta Zahara'u sun je har Katsina inda yake bautar ƙasar domin duba shi, amma aka sanar da su bai koma ba.

Shin ko garkuwa aka yi da shi?

Legit.ng Hausa ta gano cewa babu wanda yasan in da Abdurrahman yake a yanzu, kuma babu wasu kwararan hujjoji da suka tabbatar da garkuwa aka yi da shi.

Wata majiya ta tabbatar mana da cewa ba'a samu kira domin neman kuɗin fansa ba, kuma babu wata alama da ta ke nuni da garkuwa aka yi da Ɗan kwamishiniyar.

Dakta Zahara'u, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ƙara da cewa tun da Abdurrahman ya bar gida, kwanaki 11 kenan ba su ji ɗuriyarsa ba.

Kara karanta wannan

Dan Sarauniya ya kurmance a kotu, ya tilasta Alkali dage zama

A halin yanzun, jami'an tsaro a jihar Kano, sun fara bincike don nemo in da Abdurrahaman ya shiga.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda a Katsina

Wasu yan bindiga da suka yi yunkurin aikata ta'addanci a Katsina, sun kwashi kashin su a hannun gwarazan yan sanda.

Jaruman hukumar yan sanda reshen jihar sun samu nasarar dakile harin yan ta'addan kuma sun kwato dabbobin da suka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: