APC na son amfani da N3tr kudin tallafi wajen wawure makudan kudin 2023, PDP

APC na son amfani da N3tr kudin tallafi wajen wawure makudan kudin 2023, PDP

  • Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi Gwamnatin APC da kokarin amfani da kudin tallafi wajen wawuran wasu makudan kudi
  • PDP tace ta wani dalili za'a tanadi N400bn na wata shida (Junairu zuwa Yuni) amma ace N2.557 trillion ake bukata na Yuni zuwa Disamba
  • PDP ta bukaci gwamnatin tarayya ta bayyanawa kowa yadda za'a kashe kudin

Abuja - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tuhumci gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kokarin sace N3 trillion da sunan kudin tallafin man fetur.

A jawabin da Kakakin uwar jam'iyyar, Debo Ologunaba, ya saki ranar Alhamis, ya bayana cewa kudin da Gwamnatin Buhari ke bukata hannun majalisa yaudara ne, rahoton ChannlesTV.

Yayinda PDP tace ba ta adawa da biyan kudin tallafi, ta bayyana cewa ikirarin N3 trillion ake bukata rainin hankali ne ga yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Najeriya na zargin NNPC da laifin sata da noke gaskiya a kan batun man fetur

A cewar jawabin PDP:

"Jam'iyyar PDP na mamakin yadda gwamnatin APC karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin amfani da talafin man fetur wajen sace makudan kudi N3tr."
"Duk da cewa PDP ba ta adawa da biyawa yan Najeriya kudin tallafin mai, jam'iyyarmu ba zata yarda da yunkurin satan da gwamnatin APC ke kokarin yi na amfani da kudin tallafi wajen cika aljihunsu gabanin saukan da zasuyi daga mulki a 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari so yake yayi amfani da N3tr kudin tallafi wajen yakin neman zaben 2023, PDP
Buhari so yake yayi amfani da N3tr kudin tallafi wajen yakin neman zaben 2023, PDP Hoto: PDP
Asali: Getty Images

Jam'iyyar PDP ta kara da cewa tana bukatan bayanai dalla-dalla na yadda za'a yi amfani da kudin tallafin da ake bukata.

Hakazalika ta yi kira ga mambobin majalisar dokokin tarayya suyi watsi da wannan bukata saboda idan suka amince aka fitar da kudi, basu yiwa yan Najeriya adalci ba.

PDP tace:

"PDP na bukatar bayanai filla-filla kan kudin tallafi wanda ya hada kudin shigo da mai cikin kasa da barauniyar Gwamnatin APC ke bukatar N2.557 trillion."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, NNPC ta bukaci a bata N3tr kudin tallafi: Ministar Kudi

Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ta bukaci kudi N3 trillion daga wajen gwamnatin tarayya matsayin kudin tallafin man fetur na 2022 tun da an fasa kara farashin mai.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a fadar Shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswa FEC.

Ta bayyana cewa maimakon N470 billion da aka ware na kudin tallafin Junairu zuwa Yuni, yanzu za'a biya karin N2.557 trillion saboda farashin mai ya tashi a kasuwar duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng