Tinubu ya lula kasar waje ganin Likita da hutawa bayan yawon ziyarce-ziyarcen da yayi
- Bayan ziyarce-ziyarcen ta'aziyya da neman goyon baya, Tinubu ya dau hutu zuwa kasar waje
- Majiyoyi sun bayyana cewa ba'a san ainihin kasar da yaje ba amma ana kyautata zato Landan ne
- Yan Najeriya sun dade suna neman sanin ainihin shekarun Bola Tinubu da kuma yanayin lafiyarsa
Arise News ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya shilla kasar waje hutawa bayan ziyarce-ziyarcen da ya kai jaje da neman a zabesa a fadin tarayya.
An nemi Tinubu an rasa a wani taron kaddamar da kwamitocin yakin neman zabensa da akayi a Ikeja, birnin jihar Legas ranar Laraba.
Manyan jiga-jigan da suka halarci taron sun hada da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, jigogin APC, da mambobin kwamitin zaben shugabannin a jihar Legas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asiwaju Bola Tinubu ya fara ganawa da Shugaba Buhari makonnin da suka gabata inda ya sanar masa da niyyar takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Daga baya ya ziyarci tsohon shugaban kasa na Soja, Ibrahim Babangida IBB.
Hakazalika ya kai ziyarar ta'aziyya jihohin Arewa irinsu Neja, Zamfara, da Katsina inda ya bada gudunmuwan miliyoyin kudade don taimakawa iyalan wadanda aka kashe
Bayan wadannan ziyarce-ziyarcen, Tinubu ya gudu kasar waje ganin Likitocinsa da hutawa.
Yayinda wasu majiyoyi ke cewa Landan ya tafi, wasu sunce basu san ainihin inda yaje ba amma sun tabbatar ya tafi kasar waje ganin Likita.
Abinda Gwamnan Legas ya fadi a taron
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce dabarar da ta fi kowace ita ce a bar Asiwaju Bola Tinubu ya karbi shugabancin kasar nan a 2023.
Sanwo-Olu ya ce za su kawo mutane sama da 1, 500 da za su dage wajen ganin tsohon gwamna Bola Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a shekarar badi.
Gwamna Sanwo-Olu ya fadi irin mutumin da ake bukata ya karbi ragamar shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa, ya ce wannan ba kowa ba ne sai shi Tinubu.
Asali: Legit.ng