Aisha Buhari ta zabi tsohon Gwamnan Borno, ta ba shi babbar kujera a makarantar da ta gina
- Sanata Kashim Shettima shi ne shugaban majalisar da za ta sa ido a kan aikin Future Assured College
- Gidauniyar Matar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ta gina Future Assured College a Borno
- Halima Buhari-Sherrif da Farfesa Aisha Ahmed su na cikin wadanda Aisha Buhari ta ba dawainiya
Abuja - Aisha Muhammadu Buhari ta nada Sanata Kashim Shettima a matsayin shugaban majalisar da ke sa ido a kan aikin makarantar Future Assured.
Legit.ng Hausa ta ji labari Mai dakin shugaban kasar ta zabi tsohon gwamnan na jihar Borno ya rike wannan mukami a Future Assured College da ke Maiduguri.
Daya daga cikin hadiman shugaban kasa, Bashir Ahmaad ya tabbatar da wannan labari a Twitter.
Ahmaad ya ce gidauniyar Aisha Buhari Foundation ta kafa wannan makaranta domin taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su a fadin jihar Bono.
Uwargidar shugaban Najeriyar, Aisha Buhari ta rantsar da Kashim Shettima da sauran ‘yan majalisarsa mutum 10 ne a fadar Shugaban kasa a birnin tarayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An rantsar da su a Aso Villa
Da take jawabi a ranar Talata 25 ga watan Junairu 2022, Hajiya Buhari tayi kira ga wadanda aka zaba su kula da makarantar, da su dage wajen taimakawa al’umma.
“Na bi a hankali na zakulo ku a matsayin wadanda za su kula da jagorancin wannan makaranta. Aikin yana da wahala, amma na yi imani ba zai gagara ba.”
“Saboda haka ina addu’a duk mu hadu gaba daya, mu yi aiki domin cin ma burinmu na gina ‘ya ‘yanmu, mu samar masu da dama, mu raya al’ummarmu.”
- Aisha Buhari
Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto uwargidar shugaban kasar ta na godewa gwamnati da mutanen jihar Borno da kuma gidauniyar TY Danjuma.
Ragowar 'yan majalisa
Rahotanni sun ce sauran ‘yan majalisar sun hada da: Halima Buhari-Sherrif wanda za ta zama sakatare, sai Dr Muhammad Idris, Hadi Uba, da Muhammad Albishir.
Sai kuma Farfesa Bulama Kagu, Farfesa Aisha Ahmed, Hon. Asabe Vilita-Bashir, Dr Hajo Sani, Nana Liberty da Hauwa Ngoma a matsayin sauran wadanda za su sa ido.
Garba Shehu ya yi wa Ortom bulala
A ranar Talata 25 ga watan Junairu 2022, aka samu labari cewa fadar shugaban kasa ta fito, ta caccaki Gwamna Samuel Ortom bayan ya soki Muhammadu Buhari.
Garba Shehu ya dura kan gwamna Ortom kan sukar da ya yi kwanan nan. Shehu ya ce gwamnan bai iya biyan albashin ma'aikata sai caccakar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng