Neman adalci: Makashin Hanifa ya bayyana a kotu, an dage shari'a zuwa wasu kwanaki
- A yau ne aka gurfanar da mutumin nan da ya kashe dalibarsa bayan sace ta a gaban kotu don amsa laifukansa
- Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, an zauna a kotu, sannan an saurari lauyoyi kan batun nasa
- Rahoton ya ce an zauna ne a wata kotun majastare a jihar Kano, wacce ke karkashin alkali Muhammad Jibril
Jihar Kano - Shugaban makarantar Noble Kids da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Abdulmalik Tanko, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke jihar Kano.
An gurfanar da shi a gaban babban alkalin kotun, Muhammad Jibril, kan kisan gillar da ya yi wa Hanifa Abubakar, ‘yar shekara biyar, wata dalibarsa da ya sace.
Abdulmalik ya amsa laifin kashe Hanifa da gubar bera bayan ya sace ta a watan Disamba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kafar yada labarai ta BBC Hausa ta rahoto cewa, Abdulmalik ya isa kotun ne tare da wani wanda ake zarginsu da aikata laifin tare.
Waye lauyan da ke tsagin gwamnati?
A cewar rahoto, kwamishinan Sharia na Jihar Kano Barista Musa Lawan ne ke jagorantar lauyoyin gwamnati da ke neman tabbatar da adalci kan kisan Hanifa, wanda shi ne lauya mai gabatar da karar.
Idan baku manta ba, an kama Abdulmalik da wasu mutum biyu, Fatima Jibrin Musa da Hashimu, da laifin hada kai wajen sace Hanifa don neman kudin fansa da kuma kashe ta daga karshe.
Bayan sauraran batutuwa, kotu ta dage zuwa nan da kwana bakwai, inda ake sa ran za a yanke wa wadanda ake zargin hukunci daidai da laifinsu, za a kuma ci gaba da tsare Abdulmalik da abokan harkallarsa.
A bangare guda, ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana darajar kananan yara yayin da yake martani kan kisan Hanifa Abubakar a Kano.
Ministan, wanda babban malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce mutane na cin albarkacin kananan yara wajen tausaya musu da Allah ke yi.
A karatunsa na littafin Birrun Walidayya (Biyayya ga iyaye darasi na 12), wanda ya gabatar ranar Lahadi, Pantami yace a ranar Lahira lallashin ƙananan yara ake su shiga Aljanna.
Asali: Legit.ng