Aisha Buhari ta bayyana babban hukuncin da take goyon bayan a yanke wa wanda ya kashe Hanifa a Kano
- Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta nuna goyon bayanta kan irin hukuncin da ya dace a yanke wa makashin Hanifa
- Uwar gidan shugaban tace tana goyon bayan hukuncin da Shiekh Abdallah Gadon Ƙaya, ya yi kira a yanke wa mutumin
- Malamin addinin Musuluncin yace kamata ya yi a fito fili a kashe wanda ya kashe Hanifa, domin ya zama izina ga mutane
Kano - Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta shiga jerin yan Najeriya dake kiran a ɗauki tsattsauran mataki kan makasan Hanifa Abubakar.
Hanifa Abubakar yar kaminin shekara 5 a duniya, ta rasa ranta ne a hannun shugaban makarantarsu, wanda ya yi garkuwa da ita kuma ya kashe ta.
Matar shugaban ƙasa ta sanya wani gajeren bidiyo a shafinta na Instagram, wanda babban malamin addninin musulunci, Sheikh Abdallah Gadon ƙaya, yake neman a ɗauki mataki kan lamarin.
Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma
A cikin kalamansa, Malamin yace ran makashin Hanifa bai fi na wacce ya kashe ba, dan haka shi ma a kashe shi kowa ya gani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gadon Ƙaya yace:
"Dan haka kamata ya yi a kashe shi, kamar yadda ya halaka ƙaramar yarinya. Kuma idan za'a kashe shi, kamata ya yi a fito fili kowa ya gani, domin gobe kar wani ya maimaita."
Me Aisha Buhari tace kan lamarin?
Aisha Buhari ta nuna goyon bayanta kam kalaman malamin na raba makashin Hanifa da duniya, kuma ta jawo hankalin sufeta janar na yan sandan ƙasar nan.
A kalamanta, uwar gidan shugaban ƙasa tace, "Muna goyon bayan hukuncin Malam."
A ranar 2 ga watan Disamba, 2021, shugaban makarantar yara dake Kwanar Dakata, ƙaramar hukumar Nasarawa, cikin kwaryar birnin Kano, Abdulmalik Tanko, ya sace Hanifa Abubakar.
Kano: Abun da na faɗa wa Hanifa kafin ta karisa mutuwa bayan na shayar da ita guba, Shugaban makaranta
Jami'an tsaro sun samu nasarar kame Tanko, wanda ya karbi N100,000 a wani sashi na miliyan N6m da ya nema kudin fansa daga iyalan yarinyar.
Shugaban makarantar ya kashe ƙaramar yarinyar da maganin ɓera na N100 kacal, kamar yadda ya tabbatar wa hukumar yan sanda.
A wani labarin kuma gwamna Samuel Ortom, ya yafe wa wasu mutum 49 dake jiran zartar da hukuncin kisa a gidan kaso
Gwamna Ortom na jihar Benuwai, ya yafe wa wasu mutum 50, mafi yawan su, suna jirar zartar musu da hukuncin kisa ne a gidan Yari.
Mutum 49 daga ciki suna kan hanyar zartar da hukuncin kisa, yayin da ɗaya kuma aka rage masa tsawon zamansa a gidan Yari.
Asali: Legit.ng