Ka tsaye: Wasar kifa daya kwala, Tunisiya ta yi waje da Najeriya, 1-0

Ka tsaye: Wasar kifa daya kwala, Tunisiya ta yi waje da Najeriya, 1-0

Yan kwallon Najeriya Super Eagles zasu buga wasarsu na kifa daya kwala a gasar kofin nahiyar Afrika tare da yan kwallon kasar Tunisiya.

Za'a fara buga wannan wasa ne a filin wasan Roume Adjia dake garin Garoua, kasar Kamaru misalin karfe 8 na yamma.

Najeriya ta lallasa kasar Masar, Sudan, da Guinea Bissau a wasanninta na ukun farko.

Ga jerin yan wasan da aka zaba yau:

Ka tsaye: Yadda wasar kifa daya kwala ke gudana tsakanin Najeriya da Tunisiya
Ka tsaye: Yadda wasar kifa daya kwala ke gudana tsakanin Najeriya da Tunisiya
Asali: Facebook

An tashi, Tunisiya ta yi waje da Najeriya, 1-0

Wasar kifa daya kwala, Tunisiya ta yi waje da Najeriya, 1-0

Saura mintuna uku kacal, har yanzu ana cin Najeriya

Saura mintuna uku kacal, har yanzu ana cin Najeriya

An baiwa Alex Iwobi jan kati

Daga shigowarsa, Alex Iwobi na Najeriya ya samu jan kati, yanzu yan kwallo 10 zasu kara da 11. Gashi ana cin Najeriya 1

An ci Najeriya kwalla daya,

Dan wasan kasar Tunisiya, Yousef, ya zura kwallo guda ragar Najeriya ana dawowa daga hutun rabin lokaci

An dawo daga hutun rabin lokaci

Bayan hutun mintuna 15, an dawo filin wasa

An tafi hutun rabin lokaci, har yanzu shiru

Yan kwallon Najeriya sun matsawa Tunisiya lamba amma Larabawa sun kulle bayansu da kwadon karfe.

An tafi hutun rabin lokaci kuma za'a dawo bayan kimanin min 15

Minti 30 da fara wasa

An kwashe mintuna talatin da fara wasa, babu wanda ya ci kwallo tsakanin Najeriya da Tunisiya

Online view pixel