N13k ne albashinmu: Sanata ya bayyana yadda ake biyan sanatoci a 1999
- An ce Sanatocin da suka yi aiki a majalisar dokokin tarayya tsakanin 1999 da 2023 suna karbar N13,000 a matsayin albashi
- Dan majalisa kan karbi albashi ne tare da alawus din abubuwan da aka amince da su a kasafin kudi ne kawai
- Sanata Matori wanda ya yi aiki a matsayin dan majalisa a majalisar dattawan wancan lokacin ya ce babban abun da shi da takwarorinsa suke duba ba kudi bane illa soyayyarsu ga Najeriya
Tsohon dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Salisu Matori, ya bayyana cewa shi da takwarorinsa ba su samu albashi da alawus irin wanda yan majalisar dokokin kasar yanzu ke karba ba.
Punch ta rahoto cewa tsohon dan majalisar mai shekaru 80 wanda ya yi aiki a matsayin sanata mai wakiltan Bauchi ta kudu a jihar Bauchi tsakanin 1999 da 2003 ya ce sanatoci a waccan lokacin suna karbar N13,000 a matsayin albashi duk wata idan aka kwatanta da yan majalisar yanzu.
Da yake magana a kan burukansa da abun da yake yiwa Najeriya fata, Matori ya ce yana da gogewa masu ban sha'awa a yayin da ya bautawa Najeriya a matsayin dan majalisa kuma cewa hakan ya nuna a hidimar da ya yiwa kasar.
Ya bayyana cewa yan majalisa na wancan lokacin, musamman wadanda ke a majalisar dattawa sun himmatu wajen bayar da gudunmawarsu ta hanyar kawo ci gaba ga Najeriya da al’ummarta.
Matori ya ce babban abun da shi da takwarorinsu suka damu da shi shine soyayyarsu ga Najeriya, kasarsu ta gado kamar yadda kowa ke sanya tunanin kasar a gaba komai.
Matori ya ce:
"Wato babban abin da kowannenmu ya fi mayar da hankali a kai a wancan lokacin shi ne, a iya sanina, 'Najeriya farko' ba wasu abubuwa na daban ba.
"Misali idan ka duba alfanun da ake samu daga shi, idan muka shigo bangaren albashinmu N13,000 ne kacal a kowane wata kuma ba mu samu wasu alawus-alawus ba, sai alawus na wasu kayayyaki.”
Karancin albashi bai dame mu ba
Da yake magana kan yanayin da Najeriya ke ciki a wancan lokacin, Matori ya ce yan majalisa a zamaninsu basu taba gajiyawa ba wajen yiwa yan Najeriya da kasar hidima gwargwadon iyawarsu.
Ya ce:
“A daya bangaren, masu zabe, abin da suke tsammani da kwadayin abin duniya bai kai abin da muke da shi ba a yau, ka ga al’ummarmu ta kara tabarbarewa a yau ta hanyar neman abin duniya, wannan kuwa abin takaici ne matuka."
Ahmad Lawan ya fadi sirri, ya bayyana albashin sanatoci da 'yan majalisun Najeriya
A gefe guda, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, ya bayyana albashin ‘yan majalisar tarayya da kuma kudaden alawus-alawus da ake biyansu.
Lawan ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ce ya zarce magabatansa wajen amincewa da kudirin doka.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a cikin wata makala da aka gabatar a jerin lakcocin ‘yan majalisa na farko da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokuradiyya ta kasa ta shirya.
Asali: Legit.ng