Da ɗuminsa: Jirgin ƙasa ya markaɗe tirelar siminti da adaidaita sahu a Kano

Da ɗuminsa: Jirgin ƙasa ya markaɗe tirelar siminti da adaidaita sahu a Kano

  • Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya murkushe tirelar siminti tare da wata adaidaita sahu a titin Obasanjo da ke kwaryar birnin Kanon Dabo
  • Kamar yadda ganau suka tabbatar, tirelar ta tunkaro layin dogon yayin da jirgin ya taho da saurin sa, hakan yasa ya mitsike ta
  • Har a halin yanzu ba a tabbatar ko an rasa rai ba a wannan hatsarin, amma an kwashe wadanda lamarin ya shafa zuwa asibitin Murtala

Jirgin ƙasa dauke da fasinjoji ya markaɗe tirelar siminti da kuma adaidaita sahu wacce aka fi sani da Keke Napep a Kano.

Mummunan al'amarin ya auku ne a titin Obasanjo da ke ƙwaryar birnin Kano a safiyar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Da ɗuminsa: Jirgin ƙasa ya markaɗe tirelar siminti da adaidaita sahu a Kano
Da ɗuminsa: Jirgin ƙasa ya markaɗe tirelar siminti da adaidaita sahu a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ganau ba jiyau ba waɗanda ke kasuwanci a kusa da layin dogon, ya ce sun ga tirela ta na tafe kusa da dogon yayin da jirgin ƙasan ya dumfaro wurin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

Ganau ɗin ya ce sun yi ƙoƙarin ankarar da tirelar simintin amma direban bai lura ba, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har yanzu dai ba a tabbatar da cewa an rasa rai ba a wannan hatsari amma an gaggauta miƙa mutanen da lamarin ya ritsa da su zuwa asibitin Murtala Muhammad da ke Kano.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng