Kotun Italiya ta saka doka kan banɗaki mai ƙara, ta ce hakan shiga hakkin bil’adama ne

Kotun Italiya ta saka doka kan banɗaki mai ƙara, ta ce hakan shiga hakkin bil’adama ne

  • Wata babbar kotu da ke kasar Italiya ta sanya dokar bandaki mai kara musamman da dare a matsayin cutar da bil’adama
  • Hakan ya biyo bayan wata shari’ar da aka yi shekaru 19 ana yi akan wasu ma’aurata da suka kai karar makwabtan su saboda karar bandaki cikin dare
  • A cewarsu karar bandakin tana hana su bacci, hakan yasa sai da kotu ta bukaci makwabtan nasu (maza guda 4) da su biya su $565 ga ko wacce shekara tun daga shekarar da suka fara amfani da bayin

Italiya - Wata babbar kotu da ke kasar Italiya ta sanya dokar karar da bayi ya ke yi a cikin dare wanda tace hakan na cikin abubuwan da ke shiga hakkin bil’adama, The Guardian ta ruwaito.

Kotun ta koli da ke Europe ta kafa wannan dokar ne bayan kwashe shekaru 19 ana shari’a tsakanin wasu ma’aurata da ke zaune a wani gida kusa da La Spezia da suka kai karar makwabtan su akan hana su bacci saboda karar bandakin su.

Kara karanta wannan

Kisan gillar Hanifa: Gwamna Ganduje ya magantu, ya bayyana matakin da za a dauka

Kotun Italiya ta saka doka kan banɗaki mai ƙara, ta ce hakan shiga hakkin bil’adama ne
Italy: Kotu ta saka doka kan banɗaki mai ƙara, ta ce hakan shiga hakkin bil’adama ne. Hoto: Guardian NG
Asali: Twitter

Sai dai kotun bata dauki hukuncin da ma’auratan suka kai ba, hakan yasa suka daukaka kara zuwa wata kotun daukaka kara da ke arewacin birnin Genoa.

Sai da kotun ta bukaci a yi bincike akan lamarin

Daga nan kotun ta bayar da umarnin ayi bincike akan lamarin wanda binciken ya nuna tsabar karar da bayin ya ke yi.

Kamar yadda Today.ng ta ruwaito, gidan na wasu maza guda 4 ne wadanda makwabtan ma’auratan ne kuma sun makala tankin ruwa bisa wata katanga mai inci 9 wacce bata da nisa daga dakin ma’auratan.

Bayan kotun ta duba kokarin da ma’auratan suke yi kafin su samu bacci mai kyau saboda karar ruwan da bandakin yake yi, kotun ta ce hakan ya shiga hakkin bil’adama.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Sanata ta aika saƙo mai tada hankali ga Tinubu, Osinbajo, Atiku da sauran ƴan takara

Kamar yadda Alkalin kotun ya ce, yadda II Giornalr ya nuna, hakan ya ci karo da dokar kare hakkin bil’adama ta Europe na ba mutane damar yin harkokin su na yau da kullum ba tare da takura su ba.

Kotun ta nemi su biya ma’auratan makudan kudi

Kotun ta yanke hukunci tare da amfani da dokar inda ta umarci masu gidan (mazan guda 4) da su matsar da tankin ruwan su daga gefen katangar ma’auratan kuma su kirga shekarun da suka kwashe tun daga makala tankin, su biya ma’auratan $565 duk shekara, wanda hakan ya cika $10,760 na cutar dasu da suka yi.

Mazan sun bukaci sassauci ta hanyar kai kara kotun koli, amma itama ta yi hukunci kamar yadda waccen ta yi.

Kotun Europe ta kare hakkin bil’adama ta nuna muhimmancin kare hakkin mutane da kuma tabbatar da samar musu da rayuwa ba tare da takura musu ba, kamar yadda II Gionale ya nuna.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Alkalin ya kara da kafa dokar kora ruwa a salgar zamani wacce zata yi kara a matsayin hanyar cutar da makwabta kuma hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Italiya ta takura wa lafiyar mutane.

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164