Kano: Abun da na faɗa wa Hanifa kafin ta karasa mutuwa bayan na shayar da ita guba, Shugaban makaranta

Kano: Abun da na faɗa wa Hanifa kafin ta karasa mutuwa bayan na shayar da ita guba, Shugaban makaranta

  • Shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, wanda ya sace Hanifa kuma ya kashe ta, ya faɗi firar da suka yi kafin ta karisa mutuwa
  • Malamin yace ya yi amfani da robar madara ta yara 'Bobo' wajen zuba wa Hanifa guba, kuma ya yaudareta ta sha
  • Asirin malamin ya tonu ne lokacin da ya zo karɓan kudin fansa, duk da kasancewar ya kashe ɗalibar tasa

Kano - Shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary, Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe ɗalibarsa Hanifa Abubakar, ya bayyana hirarsu da ita bayan shayar da ita guba.

Tun da farko, Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Tanko ya bayyana cewa ya yi amfani da maganin ɓera na N100 wajen kashe yarinyar yar shekara 5.

Tanko, wanda shi ne shugaban makarantar da Haneefa ke karatu, yace ya ɗauki matakin kashe ta ne domin rufa ma kansa asiri kada a kame shi.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Shugaban makaranta
Kano: Abun da na faɗa wa Hanifa bayan na zuba mata guba a Shayi, Shugaban makaranta Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abin da na faɗa mata kafin ta mutu

Malamin yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na same ta a gida lokacin tana bacci kusan ƙarfe 11:00 na dare. Na gama shan shayi na, sai na tashe ta daga bacci. Na zuba ragowar shayin a cikin robar madarar yara BOBO, na zuba gubar ɓera a ciki."
"Na faɗa mata zan kaita gidan kawunta ne, kuma akan hanya ne na bata gubar kuma ta sha, daga nan sai muka shiga ɗaya daga cikin reshen makarantar mu, saboda muna da rassa biyu."
"Na shiga tare da ita bayan na faɗa mata zan ɗauki wani abu ne a ciki. Ta amince ta shiga kuma anan ne ta ƙarasa mutuwa."

Tanko, yace ya binne gawar Hanifa a cikin harabar makarantar saboda bai samu damar neman wani wuri mai tsaro da zai binne ta ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

A wani labarin kuma gwamna Samuel Ortom, ya yafe wa wasu mutum 49 dake jiran zartar da hukuncin kisa a gidan kaso

Gwamna Ortom na jihar Benuwai, ya yafe wa wasu mutum 50, mafi yawan su, suna jirar zartar musu da hukuncin kisa ne a gidan Yari.

Mutum 49 daga ciki suna kan hanyar zartar da hukuncin kisa, yayin da ɗaya kuma aka rage masa tsawon zamansa a gidan Yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262