Da duminsa: Gwamna ya dakatad da Sarakunan gargajiya hudu kan sun yi laifi
Makurdi - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya dakatad da sarakunan gargajiya a kananan hukumomin Ukum, Logo, da Katsina-Ala bisa zargin aikata laifi.
Sarakunan da haka ya shafa sune Mue Ter Ngyen, Cif D Ijah daga Ukum, Mue Ter Ichongo, Cif Terngu Iorhuna da Mue Ter Ipusu, Cif Enoch Kyumen da kuma Dagacin Tir, Cif Johnson Boi daga karamar hukumar Katsina-Ala.
Shugaban Sarakunan gargajiyan jihar Benue, Tor Tiv, James Ayatse, ba tare da bata lokaci ba ya nada mukaddasan sarakunan da zasu maye gurbinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin gargajiya, Mr. Ken Achabo, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, rahoton Vanguard.
Yace:
"Tor Tiv ya nada Cif Donald Vihive a matsayin Mue Ter Ngyen; Cif Stephen Tyokpev matsayin Mue Ter Ipusu da Cif Orlu Mbakor, matsayin Ter Chongo."
Jawabin ya kara da cewa Tor Sankera, Cif Abu King Shuluwa, kuma ya nada Philip Saamaaya matsayin mukaddashin dagacin Tir, a Katsina-Ala.
Asali: Legit.ng