Yan bindiga sun sake kai harin rashin imani, sun halaka dandazon mutane a Neja
- A makon nan, gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya bayyana cewa an kai hari aƙalla 50 jiharsa tun bayan shigowar sabuwar shekara
- Wasu tssgerun yan bindigan sun sake kai hari ƙauyen Bobi dake jihar, inda suka kashe dandanzon mutanen da ba'a gano adadin su ba
- Kwamishinan yaɗa labarai na jihar yace gwamnati na bakin kokarinta wajen kawo karshen ayyukan yan ta'adda a faɗin jihar
Niger - Wasu miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari na rashin imani ƙauyen Bobi, dake ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja.
Rahoton da The Nation ta tattara ya bayyana cewa maharan sun kashe dandazon mutane da har yanzun ba'a gano adadin su ba.
Yan bindigan sun farmaki ƙauyen ne a kan babura, kowanne daga cikin su na ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.
Da farko maharan sun shiga kasuwar Nkuru, yayin da mutane yan kasuwa da masu siya ke gudanar da harkokinsu, amma ƙarar harbin bindiga ta sanya kowa ya watse daga kasuwar.
Daga nan, sai maharan suka shiga ƙauyen, duk mutumin da suka haɗu da shi sai sun halaka shi, kuma suka ƙona gidajen mazauna garin.
Gwamnati ta tabbatar da harin
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, ya tabbatar da kai mummunan harin.
Ya kuma bayyana cewa har zuwa yanzun hukumomin ba su tantance adadin yawan mutanen da suka rasa rayuwarsu a harin ba.
Kazalika, kwamishinan ya ƙara da cewa yan bindiga sun ƙona da yawa daga cikin gidajen mazauna ƙauyen.
Punch ta rahoto ya ce:
"Mutanen da ba'a san yawan su ba sun rasa rayuwarsu a harin, kuma bayan haka maharan sun ƙona gidaje."
Idris yace yan bindigan da suka kai harin, suna daga cikin waɗan da suka gudo daga luguden wutan sojoji a jihohin Zamfara, Kaduna, Kebbi da Sokoto.
Wane mataki gwamnatin Neja ke ɗauka?
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin Neja na kawo ƙarshen ayyukan ta'addancin yan bindiga a faɗin jihar.
A wani labarin na daban kuma Yan sanda sun yi magana kan wurin da Bello Turji ya koma bayan tserewa daga Zamfara
Rundunar yan sanda ta jihar Kwara ta musanta ikirarin ɗan majlisar wakilan tarayya game da gawurtaccen ɗan bindiga, Bello Turji.
Ɗan majalisar da ya yi wannan furuci, ya bayyana cewa luguden wutan sojojin Najeriya ya sa Turji ya tsere daga Zamfara, ya kafa sansani a dajin Kwara.
Asali: Legit.ng