Duk da biyan kudin fansan N6m, masu garkuwa sun kashe yarinyar da suka sace a Kano

Duk da biyan kudin fansan N6m, masu garkuwa sun kashe yarinyar da suka sace a Kano

  • Yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano da aka sace a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya ta mutu
  • Kawunta Zubair Siraj ya bayyana cewa guba suka sanya mata a abinci bayan karbar kudin fansa
  • An damkesu yayinda suke kokarin kara karban wani sabon kudin fansa karo na biyu

Kano - Duk da karban kudin fansa milyan shida (N6million), masu garkuwa da mutane sun hallaka Hanifa Abubakar, yarinya 'yar shekara biyar da suka sace a Kano.

Kawunta, Suraj Suleiman, wanda ya tabbatar da kisan yace sun samu gawarta cikin wata makaranta a unguwar Tudun Wadan jihar Kano, rahoton DailyNigerian.

A cewarsa, wanda ya saceta matarsa ya fara kaiwa yarinyar ta ajiye masa amma ta kiya.

Yace:

"Mutumin ya fara kai Hanifa wajen matarsa amma taki ajiye ta. Daga nan sai ya kai ta TudunWada inda yake da wata makaranta, sannan ya sanya maganin bera cikin shayi ya bata."

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano

"Bayan ta mutu, masu garkuwan suka yi mata gunduwa-gunduwa sannan suka birneta cikin makarantar."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da biyan kudin fansan N6m, masu garkuwa sun kashe yarinyar da suka sace a Kano
Duk da biyan kudin fansan N6m, masu garkuwa sun kashe yarinyar da suka sace a Kano Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

An tattaro cewa an damke masu garkuwan a Zaria Road, Kano da daren jiya yayinda suke kokarin kara karban wani kudin fansa.

Lokacin da aka sace Hanifa

A ranar Asabar, 4 ga Disamba, 2021, kun ji cewa an sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar a unguwar Kawaji da ke Kano.

Masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da ita a cikin babur din dai-daita sahu yayin da suka yaudare ta da sunan rage hanya

Daily Nigerian ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da karfe 5 na yamma lokacin da yarinyar da sauran yaran unguwar suke dawowa daga makarantar islamiyya.

Unguwar Kawaji a karamar hukumar Nassarawa na daya daga cikin unguwannin da ake fama da matsalar satar yara a Kano.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma

A cikin unguwar a baya, an yi garkuwa da Yusuf Nasiru dan shekara 9 a ranar 28 ga watan Disamba, 2020 bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng