Karya ne: NEC ba ta kai ga kara kudin man fetur daga N165 zuwa N300 ba - Osinbajo
- Jita-jitar cewa majalisa NEC ta amince a kara farashin man fetur zuwa sama da N300 ba gaskiya ba ne
- Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya karyata wadannan rahotanni
- Shugaban gwamnoni, Kayode Fayemi ya ce ba su da hurumin da za su yanke farashin da za a saida mai
Abuja - Rahotanni su na ta yawo a makon nan cewa majalisar tattalin arziki ta NEC, ta bada shawarar a kara farashin litar man fetur zuwa N302.
Fadar shugaban kasa ta fito ta musanya wannan zargi, ta ce kawo yanzu ba a dauki matsaya ba.
Mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya fitar da gajeren jawabi a shafinsa na Twitter, inda ya karyata wannan rahoto.
Da yake magana a ranar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022 da karfe 2:16 a Twitter, Akande ya tabbatar da NEC ta na zama a kan batun tallafin fetur.
Sai dai zuwa lokacin da ya yi wannan jawabi, hadimin Farfesa Yemi Osinbajon ya ce ba a tsaida magana ba tukun, har kuma a ce an kawo sabon farashi.
Akande ya yi kira ga manema labarai su rika tuntubarsu kafin su fitar da irin wadannan rahoton. Jaridar Tribune ta fitar da makamancin wannan labarin.
“Ko da cewa babu shakka ana tattaunawa a game da batun tallafin man fetur, amma babu lokacin da aka cin ma matsaya kamar yadda wannan rahoton yake ikirari.”
“Za a fi fitar da rahoto mai kyau ga mutane idan ana tuntubar wadanda abin ya shafa a game da abubuwa masu irin wannan muhimmanci.” – Laolu Akande (@Akandeoj)
Babu ruwan mu - NGF
Haka zalika shi ma shugaban gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya karyata rahotannin da suke yawo, ya ce ba gwamnoni ke da alhakin tsaida farashi ba.
An rahoto Gwamna Kayode Fayemi yana cewa gwamnoni su na cikin wadanda ake tattauna da su, amma ba su ce a maida litar man fetur ya koma N302 ba.
Gwamnoni za su yi zama da NLC, TUC
Dazu aka ji cewa Dr. Kayode Fayemi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnoni na NGF ya bayyana yadda ake ciki a kan maganar kara farashin mai.
Gwamnoni 36 na tarayyar Najeriya sun amince su tattauna da shugabannin kungiyoyin NLC na ‘yan kwadago da na ‘yan kasuwa domin a samu maslaha.
Asali: Legit.ng