Babban Sarki ya shawarci Buhari ya dawo da shirin WAI, da hukuncin kisa ga ƴan ta'adda da matsafa

Babban Sarki ya shawarci Buhari ya dawo da shirin WAI, da hukuncin kisa ga ƴan ta'adda da matsafa

  • Basaraken kasar Iwo, HRM Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi ya bukaci gwamnatin tarayya bisa shugabancin Muhammadu Buhari ta yanke hukuncin kisa ga wasu masu laifuka da ya zayyano
  • A cewarsa matsawar aka kama mai safarar miyagun kwayoyi, matsafa da kuma duk wasu ‘yan ta’adda a halaka su don hakan zai taimaka wurin gyara akan tsaro
  • A cewarsa shan miyagun kwayoyi ne ya ke janyowa ‘yan ta’adda su na aikata miyagun laifuka ba tare da imani ba, don haka kada a saurara wa masu safarar su

Fitaccen basaraken kasar Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yanke wa duk wani mai safarar miyagun kwayoyi, matsafi ko dan ta’adda hukuncin kisa don kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Vanguard ta ruwaito.

Oluwa ya ce wannan dokar za ta taimaka wurin dakatar da wasu daga shiga irin wadannan miyagun harkokin.

Kara karanta wannan

Shari'ar Nnamdi Kanu: Mai gidan jaridar Sahara Reporters ya gamu da fushin 'yan sanda

Babban Sarki ya shawarci Buhari ya dawo da shirin WAI, da hukuncin kisa ga ƴan ta'adda da matsafa
Oluwa na Iwo ya shawarci Buhari ya dawo da shirin WAI, ya kuma saka hukuncin kisa ga 'yan ta'adda da matsafa. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

A cewarsa, sai ‘yan ta’adda sun sha miyagun kwayoyi sun yi tatil kafin su iya ayyukan rashin imani kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hakan yasa ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki tsauraran matakai akan duk wasu masu harkar kwayoyi, inda ya ce a koma amfani da shirin yaki da rashin tarbiyya (WAI) wacce gwamnatin soji ta Janar Muhammadu Buhari da Tunde Idiagbon ta kaddamar a 1984.

An fara shirin WAI ne a 1984

Shirin WAI ya fara ne a watan Maris din 1984 kuma an ci gaba da amfani da shi har watan Satumban 1985.

Oluwa ya ce hakan ya samar da mutanen kirki a gari wanda jami’an tsaro suka dinga yaki da munanan dabi’u.

Ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya zartar da manyan hukunce-hukunce ga ‘yan bindiga da masu safarar miyagun kwayoyi wanda ke janyo kashe-kashen ‘yan Najeriyan da basu ji ba basu gani ba.

Kara karanta wannan

Mai shari'a ta caccaki DSS, ta ce ka da su kara kawo Nnamdi Kanu gaban kotu da kaya daya

Ya bayyana wannan bukatar tashi ne ta takardar da sakataren watsa labaran sa, Alli Ibraheem, ya saki wacce ta zo kamar haka:

“Rashin tsaron da ke Najeriya ya yi yawa. Na karanta labarin yadda ‘yan bindiga suka taso jihar Zamfara da hare-hare. Hakan ya na da ban tausayi da cin rai. Rashin daukar matakai ne ga masu laifuka ya ke janyo ci gaban harin.”

Miyagun kwayoyi ne tushen ta’addanci

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta bayyana:

“Yan ta’adda su kan aikata laifukan ne bayan sun sha miyagun kwayoyi, a lokacin imaninsu ya tafi kuma ba sa cikin hayyacin su. Don haka ya kamata gwamnati ta dauki manyan matakai.
“Najeriya tana cikin matsala, dillalan miyagun kwayoyi, matsafa, ‘yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane wadanda suka tasa kowa gaba. Arewa tana fama da ta’addanci yayin da kudu take fama da matsafa. Babu ranar da zata wuce babu mummunan labari.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Ya ce hakkin gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma hakan yasa ya ga ya kamata a dawo da shirin WAI wacce za ta taimaka wurin tsoratar da masu shirin shiga ta’addanci.

Idan ba a yi hakan ba, a cewarsa, kasa za ta ci gaba da shiga garari kowa yana yin abinda ya ga dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164