Daga karshe: Kotu ta yi hukunci tsakanin Nnamdi da gwamnati, an ci gwamnati tara
- A wani bangare na shari'ar Nnamdi Kanu da gwamnatin tarayya, an yi hukunci kan batun da ya shafi kutsawa gidan Kanu
- A baya sojojin Najeriya sun taba shiga neman Nnamdi a gidansa a 2017, lamarin da bai yiwa Kanu dadi ba
- An yi hukunci, an ce gwamnati ta biya shi diyyar shiga gidansa na N1bn, tare da neman afuwar Kanu a gidajen jaridu
Umuahia, Abia - Wata babbar kotu a Umuahia ta umurci gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya da su biya shugaban 'yan IPOB, Nnamdi Kanu N1bn bisa laifin mamaye gidansa a watan Satumban 2017, Vanguard ta rahoto.
Hakazalika, an umarci gwamnatin tarayya da Sojoji da su nemi gafarar Kanu bisa take masa hakkinsa na dan adamtaka.
Mai shari’a Benson Anya ya bayar da wannan umarni ne a yau a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da Kanu ya shigar a kan gwamnatin tarayya da sojoji da sauran su.
Mai shari’a Anya ya bayyana mamayar gidan Kanu na Afaraukwu a matsayin abin kyama kuma rashin kunya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sai dai ya yi fatali da wasu bukatun da kungiyar lauyoyin Kanu ke nema, ciki har da dawo da shi gida daga Kenya da kuma ci gaba da tsare shi a hannun hukumar DSS.
Mai shari’ar ya kuma amince da bukatar da kungiyar lauyoyin Kanu ta nema, inda ya umarci Gwamnatin Tarayya da ta nemi gafara a cikin jaridun kasar nan guda uku kan farmakin da aka kai gidan Kanu na Afaraukwu.
Ya kuma shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi duba ga wani kuduri na siyasa wajen tunkarar dambarwar da ta shafi Kanu.
An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci tsakanin Kanu da gwamnati
A farko, jami’an tsaro dauke da muggan makamai sun tare hanyoyin da ke kaiwa harabar babbar kotun jihar Abia da ke kan titin Ikot Ekpene a Umuahia yayin da kotu za ta yanke hukunci a yau kan karar da shugaban IPOB, Mazi Nnamdi ya shigar kan gwamnatin tarayya.
Tun da karfe 7:00 na safe, an baza jami'an tsaro a kusa da harabar kotun, Vanguard ta rahoto.
Haka kuma an killace dukkan hanyoyin da ke kai wa ga kotun, wanda hakan ya tilastawa masu ababen hawa da masu tafiya a kafa bin wasu hanyoyin daban-daban.
Asali: Legit.ng