Abin da ya sa ake zargina da satar kudin NPA - Hadiza Bala Usman ta fito, tayi magana
- Hadiza Bala Usman ta karyata rahotannin da ke yawo na cewa ta karkatar da dukiyar gwamnati
- Tsohuwar shugabar hukumar ta NPA ta ce zargin ta ki maidawa gwamnati wasu kudi, ba gaskiya bane
- A wani jawabi da ta fitar, Hadiza Bala Usman ta kalubalanci masu yada wannan labari su fito da hujjoji
FCT, Abuja - Tsohuwar shugabar hukumar NPA ta kasa, Hadiza Bala Usman ta kalubalanci duk wanda yake da hujja ya nuna ta karkatar da dukiyar gwamnati.
Jaridar The Cable ta rahoto Hadiza Bala Usman ta bayyana wannan ne a wani jawabi na musamman da ta fitar a ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022.
Hadiza Bala Usman ta ce ya zama dole tayi wannan bayani domin ta wanke kan ta daga zargin cewa NPA ta ki maida kudi cikin asusun gwamnati a lokacinta.
“Rade-radin da ake yi na zargin cewa mai binciken kudi ya yi magana a kan wasu kudi da kamfanonin jigila su ke bin hukumar NPA bashi ya zo gare ni.”
Za a bata mani suna - Bala Usman
“A ka’ida ya kamata hukumar NPA ta fito tayi magana ne a kan wadannan zargi, a dalilin haka ne na ki cewa komai a lokacin da labaran suka fara bayyana.”
“Sai dai ya na kara bayyana cewa burin masu yada wadannan labari shi ne kurum bata mani suna.”
Rahoton da yake yawo
“Misali a safiyar ranar Talata mutane da-dama suka turo mani wani labari a shafin sada zumunta mai taken: “NPA Audit indicts Hadiza Bala Usman for not remitting N40b, $921.61m and £289.931.82 to federal government accounts.”
A wannan rahoto an yi ikirarin an samu Hadiza Bala Usman da laifin kin zuba N40b, $921.61m da £289.931.82 da NPA ta samu zuwa ga asusun gwamnatin tarayya.
“Ina mai fada da babbar murya cewa wannan ba gaskiya ba ne, kuma kanzon-kurege ne daga duk wanda yake yada wannan karya.”
Ba haka abin yake ba
Bala Usman tace maganar gaskiya ita ce ko akwai kudin da ba a maida asusun gwamnati ba, za su tsaya ne a cikin asusun TSA inda duk kudin-shigar gwamnati suke.
Bala Usman ta kalubalanci duk mai wata hujjar wannan zargi, ya fito ya bayyanawa Duniya.
Shari'ar Alpha Beta
An ji labari tsohon babban manajan kamfanin Alpha Beta Consulting, Dapo Apara, Bola Tinubu da Akin Doherty, za su sasanta a maimakon cigaba da shari’a a gaban kotu.
Dapo Apara ya shigar da karar Bola Tinubu, yana zarginsa da satar kudi daga kamfanin Alpha Beta.
Asali: Legit.ng