Za ayi sulhu tsakanin Bola Tinubu da wanda ya kai shi kotu da zargin satar Naira Biliyan 20
- Dapo Apara ya shigar da karar Bola Tinubu, yana zarginsa da satar kudi daga kamfanin Alpha Beta
- Tsohon shugaban na Alpha Beta ya na zargin Tinubu da hannu a tsige shi saboda bankado asirinsa
- Lauyan da Apara ya dauka haya, Ebun-Olu Adegboruwa ya nuna za su janye karar da aka shigar
Lagos - Tsohon babban manajan kamfanin Alpha Beta Consulting, Dapo Apara, Bola Tinubu da Akin Doherty, za su sasanta a maimakon cigaba da shari’a a kotu.
A halin yanzu Akin Doherty shi ne shugaban kamfanin, kuma har da shi ake shari’a a gaban kotu.
Punch ta kawo rahoto a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2022 wanda ya nuna cewa za a janye karar da aka shigar, domin a sasanta ba tare da Alkali ta shiga ba.
Lauyan wanda ya shigar da kara, Ebun-Olu Adegboruwa SAN ya bayyana wannan a lokacin da aka yi zaman kotun a filin Tafawa Balewa Square da ke garin Legas.
Mun sanar da Tinubu - Lauya
Adegboruwa SAN ya shaidawa Alkalin babban kotun cewa an je an sanar da Bola Tinubu game da wannan shari’a har gidansa a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bola Tinubu ya samu labari ne ta sakon DHL da aka kai gidansa da ke titin Bourdillon a Ikoyi, Legas. Kotu ta kuma tabbatar da wannan ikirari da lauyan ya yi.
...amma za mu sasanta a waje
Adegboruwa ya kuma shaidawa Alkali mai shari’a sun zauna da sauran lauyoyin da ake wannan shari’a da su, da nufin a samu maslaha ba tare da an yi shari’ar ba.
A karshe an cin ma matsaya kamar yadda lauyan ya shaidawa kotu a zaman da aka yi a jiya.
Rahoton ya ce babu mamaki wannan maslaha da aka samu ne ya sa ba a ga wanda ake kara da lauyoyinsu a cikin kotu yayin da aka zo domin sauraron karar ba.
Aishat Opesanwo ta dage kara
Lauyan ya bukaci a kara masu lokaci domin su kammala magana. Tuni dai mai shari’a, Aishat Opesanwo ta amince da wannan bukata, ta daga wannan sharia.
Opesanwo ta ce za a dawo kotu a ranar 24 ga watan Maris, 2022 domin jin matakin da za a dauka.
Hawa na mulki ikon Allah ne - Osinbajo
Kwanaki aka ji Yemi Osinbajo yana cewa abin da ya faru da shi a 2015 ikon Allah ne, domin ba zai iya lashe zaben karamar hukuma ba, sai ga shi a fadar shugaban kasa.
Osinbajo ya ce ya na otel da abokan aikinsa, su na shirya kara da za a shigar a kotun koli, kwatsam sai aka kira shi a waya cikin dare, daga nan kuma sai labari.
Asali: Legit.ng