Garba Shehu: Buhari ya karya lagon rashawa shi yasa 'yan siyasa ke jin haushinsa

Garba Shehu: Buhari ya karya lagon rashawa shi yasa 'yan siyasa ke jin haushinsa

  • An bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban da ya yi nasarar karya lagon almubazzaranci da dukiyar kasa
  • Wannan bayanin ya fito ne ta bakin babban mai ba Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu
  • Shehu ya ce tsarin Shugaba Buhari yana da tsauri kuma zai yi wuya kowa ya wargaje shi duba da irin mutuncinsa

Birnin Tarayya, Abuja - Babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a ranar Talata, 18 ga watan Janairu, ya ce abubuwan da shugaban kasa zai bari suna da matukar tasiri.

Shehu ya kuma yi gargadin cewa da wuya wani ya iya wargaza abubuwan alherin da shugaba Buhari ya gina a tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Zaman lafiya ya samu: Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa

Garba Shehu ya fadi yadda mutuncin Buhari yake
Garba Shehu: Buhari ya karya lagon rashawa shi yasa 'yan siyasa ke jin haushinsa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Vanguard ta ruwaito cewa, Shehu, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, ‘yan siyasa da dama a kasar nan wadanda muradin su na wawure dukiyar al’umma ne jira suke wa’adin shugaban kasa ya zo karshe.

Ya ce wadannan ’yan siyasa suna muradin samun “zamanin irin na da” da za su taimaka wa kansu wajen yin sama da fadi da kudaden da aka ware don bukatun kasa.

Shehu ya ce:

"Duk da cewa shugaban kasa zai yi sauka bayan zaben wanda zai gaje shi a shekara mai zuwa - ko wanda zai gaje shi ya rayu daidai da ma'auni da misalin da ya kafa ko a'a - abin da zai bari yana da karfi kuma zai yi matukar wahala a wargaza."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: IBB ya bayyana wanda zai iya gadar shugaba Buhari

Jaridar Sun ta ruwaito cewa Shehu ya kara da cewa daya daga cikin manyan nasarorin da shugaba Buhari ya samu shine karya imanin cewa shugabanni suna karbar mulki a Najeriya ne domin su arzuta kansu.

“Wannan mugun sihiri an karya shi da kyakkyawar manufa. Kuma ya tunzura ‘yan siyasa a ko’ina. Sun yi tunanin kasar ke bibiyarsu alhalin jama'a ne ke azurta kasar."

Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari ba, Dattawan Arewa

A wani labarin, gabanin zaben 2023, kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa yankin Arewa zata zabi dan takaran shugaban kasa mai ikon sauya lamuran tattalin arzikin kasar da tsaro ba tare da la'akari da yankin da ya fito ba.

Dattawan sun ce ba zasu sake zaben dan takara bisa kabilanci kamar yadda suka zabi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ba.

Dattawan sun bayyana cewa Shugaba Buhari abin kunya ne ga Arewa da Najeriya gaba daya.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Filato: Kada wata kungiya ta dauki doka a hannunta, in ji Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.