Da sauran rina a kaba: Shekaru 6 da kawo TSA domin hana sata, har gobe ana tafka barna

Da sauran rina a kaba: Shekaru 6 da kawo TSA domin hana sata, har gobe ana tafka barna

  • Gwamnatin tarayya ta dabbaka tsarin TSA da nufin rage sata a gwamnati da tabbatar da gaskiya
  • Shekaru shida da kawo wannan tsari, bincike ya nuna har yanzu wasu ma’aikatan su na yin satarsu
  • Ana ikirarin gwamnati ta san da irin barnar da ake yi, amma ta gagara daukar matakin da ya dace

Abuja - Shekaru shida kenan da fara amfani da tsarin TSA gadan-gadan domin a tabbatar da gaskiya da rage cin dukiyar al’umma, da samun kudin-shiga.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi, ya nuna har yanzu akwai sauran aiki domin ana cigaba da wawurar dukiyar kasa a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Tun 2004 aka fara kawo maganar TSA, amma ba a dabbaka shi da kyau ba sai a 2015. Kafin wannan lokaci, ma’aikatun gwamnati su na da asusu barkatai.

Kara karanta wannan

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

Shugabannin hukumomi da cibiyoyin gwamnati su kan ci wadannan kudi ba tare da an sani ba.

Da sauran aiki

Binciken da jaridar ta gudanar ya bayyana cewa har gobe TSA bai dakatar da wawurar kudin da ake yi daga Baitul-mali ba, ana tafka satar kuma ba ta wasa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu jami’an gwamnati da aka zanta da su, sun bayyana cewa ma’aikata sun gano yadda za su kewaye TSA, su lakume kudin gwamnati ba tare da an farga ba.

Buhari
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abin da ake yi a yau

Dabarar da aka fi amfani da ita a yau ita ce, ana amincewa a aika kudi cikin asusun bankin ma’aikata a karkashin manhajar GIFMISS, sai a sulale da kudin.

A irin haka wasu shugabannin hukumomin sun karkatar da miliyoyi daga asusun ma’aikatunsu.

Wani jami’in gwamnati ya fadawa jaridar cewa TSA ba ta taimaka wajen inganta gaskiya a wurin aiki ba, canjin da aka samu kawai shi ne tattara kudi a wuri guda.

Kara karanta wannan

Ma’aikata sun fara salati, Gwamnatin Buhari za ta karbi aron N620bn daga asusun fansho

Haka zalika wani ma’aikaci a ofishin babban akawun gwamnatin Najeriya, ya ce sun gano wasu manyan ma’aikatan gwamnati su kan yi wasa da hankalin TSA.

Idan ba wajen biyan kudin ayyuka da manyan cefane ba, ana tura kudi ne cikin asusun ma’aikatan gwamnati, ya ce ana lafta kudin domin a samu na sata.

A irin haka, jami’ai suke satar dukiyar Baitul-mali cikin ruwan-sanyi. A cewar jami’in, hukuma ta gano badakalar da ake yi, amma ta gagara daukar wani mataki.

Jega ya ce ya kamata ayi gyara

Tsohon shugaban hukumar gudanar da zabe na kasa, Attahiru Jega ya ce dace ayi watsi da kudirin zabe gaba daya ba saboda an samu wasu ‘yan kura-kurai a cikinsa.

Farfesa Attahiru Jega yana ganin zai yi kyau a gyara dokar zabe domin a fara shiyawa 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng