Kai tsaye: Yadda wasar kwallon AFCON tsakanin Najeriya da Sudan ke gudana
Yan kwallon Najeriya Super Eagles zasu buga wasarsu na biyu a gasar kofin nahiyar Afrika tare da yan kwallon kasar Sudan, Falcons.
Za'a buga wannan wasa ne a filin wasan Roume Adjia dake garin Garoua, kasar Kamaru misalin karfe 5 na yamma.
Najeriya ta lallasa kasar Masar a wasarta ta farko da ci guda mai ban haushi.
Ga jerin yan wasan da aka zaba:
An tashi, Najeriya ta ci Sudan 3-1
Najeriya ta lallasa kasar Sudan a wasar kwallon AFCON da ci uku da daya
Sudan ta samu fenariti, ta rama kwallo guda
Kasar Sudan ta samu zira kwallo guda
Najeriya ta zura kwallo ta uku
Dan kwallon da ya addabi Masar a wasan farko, Moses Simon, ya zura kwallo ta uku
An tafi hutun lokaci, Najeriya na ci 2,0
Yayinda aka tafi hutun lokaci, Najeriya ta zura kwallaye biyu ragar Sudan
Najeriya ta zura kwallo ta biyu
Dan wasan Union Berin a Jamus, Taiwo Awoniyi, ya zurawa Suna kwallo ta biyu
Najeriya ta zura kwallon farko, 1-0
Samuel Chukweze ya zura kwallon farko a daidai minti uku bayan fara wasa
An fara
Kasar Sudan ce ta fara taka leda
Ana dab da farawa, yan wasan Najeriya na motsa jiki