Dalilin da yasa na ki aure tun bayan mutuwar Maryam Babangida, IBB
1 - tsawon mintuna
- Janar Ibrahim Babangida ya sake hira da yan Najeriya kan abubuwa da dama, ciki har da rashin aurensa
- Babangida, tsohon shugaban kasan mulkin Sojan Najeriya ne wanda yayi mulki tsakanin 1985 da 1993
- Bayan sama da shekaru 12 da mutuwar matarsa Maryam Babangida, har yanzu tsohon Sojan bai yi aure ba
Minna - Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya bayyana dalilin da yasa bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa, Hajiya Maryam Babangida.
IBB, wanda shekarunsa 80 yanzu ya bayyana hakan a hirarsa da sabuwar gidan talabijin Trust TV.
Allah ya yiwa Hajiya Maryam Babangida.rasuwa ranar 27 ga Disamba, 2009, tana mai shekaru 61.
Ta rasu ne a jami'ar California dake Amurka bayan fama da cutar kansa.
Yayinda aka tambayesa kan shin me yasa bai yi aure tun lokacin ba, yace:
"A'a, ban yi ba. Kuma da kun sani. Yan jarida na bibiya ta. Zabi na kenan; na yanke shawaran karramata ta hanyar kin yin wani aure."
Asali: Legit.ng