Karfin Hali: Hukumar EFCC ta damke Janar din Soja na Bogi
1 - tsawon mintuna
- Jami'an hukumar EFCC na jihar Legas sun cika hannu da wani Sojan Bogi wanda yace shi Buhari yaso ba Shugaban Sojin Najeriya
- Jami'an suna zarginsa da yin damfarar milyan dari biyu da saba'in
- Ya damfari wani kamfani da sunan zai yi amfani da kudin wajen neman shafa'a wajen Shugaba Buhari
Abuja - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta damke wani Janar din Soja na karya kan zargin damfarar N270m (Milyan dari biyu da saba'in).
EFCC ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki tare da hotunan Sojan a shafinta na Tuwita.
Sojan Bogin mai suna Bolarinwa Oluwasegun ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari ya so ya zama Shugaban hafsan Sojin Najeriya.
EFCC tace:
"Jami'ar hukumar EFCC na shiyar Legas sun damke, Bolarinawa Oluwasegun, wani Janar din Sojan karya wanda yayi ikirarin Buhari ya zabeshi matsayin Shugaban hafsan Soji da zargin damfarar N270m."
"Mutumin ya ce shi Janar ne a hukumar Sojin Najeriya kuma ya fadawa kamfanin Kodf Clearing Resources cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya katabta sunansa da na wani cikin wadanda za'a nada Shugaban hafsan Sojin Najeriya, kuma yana bukatan kudi ne don tabbatar an bashi mukamin."
Duk yunkurin da Legit Hausa tayi na samun karin bayani daga wajen hukumar EFCCC ya ci tura.
Asali: Legit.ng
Tags: