Da Dumi-Dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Ogun, ya kaddamar da babbar hanya

Da Dumi-Dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Ogun, ya kaddamar da babbar hanya

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fara ziyarar aiki ta kwana ɗaya a jihar Ogun ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, 2022
  • Buhari ya kaddamar da sabuwar hanyar Ijebu-Ode – Epe mai tsawon kilomita 14, wacce ta haɗa jihar Ogun da jihar Legas
  • Haka nan shugaban zai kaddamar da wasu sabbin jerin gidaje da gwamnatin jihar ta kammala, kuma zai halarci taron masu ruwa da tsaki

Ogun - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya isa jihar Ogun, a wata ziyarar aiki ta kwana ɗaya, da zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamna Dapo Abiodun, ya aiwatar.

Shugaban ƙasan, wanda ya yi shigar Agbada, ya isa Gateway City Gate Monument, tare da gwamna Dapo Abiodun, na jihar, da misalin ƙarfe 11:37 na safiyar Alhamis.

Buhari ya samu kyakkyawan tarba daga gwamnonin jihohin Yobe, Ekiti, Ondo, da kuma Osun, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Shugaban kasa Buhari a Ogun
Da Dumi-Dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Ogun, ya kaddamar da babbar hanya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tuni shugaban ƙasa, Buhari, ya kaddamar da sabuwar babbar hanya mai tsawon kilomita 14, wacce ta taso daga Ijebu-Ode zuwa Epe, kuma ta haɗa Ogun da Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban zai wuce kai tsaye ya kaddamar da hanyar Sagamu Interchange - Abeokuta mai tsawon kilomila 42, kuma yanzu an canza mata suna zuwa, "shugaba Muhammadu Buhari Expressway'

Sauran ayyukan da Buhari zai kaddamar a Ogun

Sauran manyan ayyukan da aka tsara shugaba Buhari zai kaddamar sun haɗa da, sabbin gidaje Kobape Housing Estate, dake a Sagamu-Abeokuta, kamar yadda Punch ta rahoto.

Sai kuma sabbin gidaje rukuni na farko dake Kings Court Estate a Abekuta, babban birnin jihar Ogun, wanda hukumar zuba hannun jari ta jihar Ogun ta gina.

Kazalika yayin wannan ziyarar, shugaba Buhari zai halarci taro a Town Hall, inda ake tsammanin zai gana da masu ruwa da tsaki da shugabannin APC reshen jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Zulum: Mayakan ISWAP sun fi na Boko Haram makamai, dole ne a dakile su

A wani labarin na daban kuma Gwamna ya sa ladan miliyan N5m kan duk wanda ya fallasa yan bindiga a jiharsa

Gwamnan jihar Imo, ya sa ladan miliyan N1m da N5m kan duk wani mutum da ya fallasa bayanai aka kama ɗan bindiga ko aka gano maɓoyarsu.

Hope Uzodinma, yace yan bindiga sun tafka aika-aikata, amma gwamnatinsa ta ɗauki matakan kawo ƙarshen su baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262