Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

  • An sace wasu daliban makaranta a sabon harin da yan bindiga suka kai gidajen daliban a jihar Plateau
  • Rahotanni sun nuna cewa akalla dalibai biy zuwa uku akayi awon gaba da su ranar Laraba
  • Jami'an Soji sun bazama cikin daji don ceti daliban

Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da akalla dalibai mata biyu na kwalejin fasahar jihar Plateau a harin da suka kai da yammacin Laraba, 12 ga Junairu, 2022.

TVC ta ruwaito cewa yan bindiga sun dira gidajen kwanan dalibai dake wajen makaranta inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi kafin sukayi awon gaba da dalibai biyu.

Jami'an Sojoji na rundunar Operation Safe Haven sun bibiyi yan bindiga don ceto daliban, rahoton ya kara.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ceto daliban Plateau Poly da yan bindiga suka sace

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai
Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sake hallaka Bayin Allah a wani danyen harin tsakar dare

A bangare guda, kungiyar Irigwe Development Association ta koka kan kisan mutanenta da ta ce an yi a kauyen Ancha, yankin Miango a karamar hukumar Bassa.

Rahoton da muka samu a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2021 shi ne an kashe mutum 18 a Ancha a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kasar Rigwe.

Mai magana da yawun bakin kungiyar Irigwe Development Association, Mr. Davidson Malison ya aikawa jaridar Vanguard jawabin da suka fitar bayan harin.

A jawabin na Davidson Malison, ya ce da kimanin karfe 12:00 na daren ranar Talata ne ‘yan bindiga suka duro kauyen Ancha, suka yi mummunan ta’adi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng