Bayan rikici ya lafa a Filato, an sake hallaka Bayin Allah a wani danyen harin tsakar dare

Bayan rikici ya lafa a Filato, an sake hallaka Bayin Allah a wani danyen harin tsakar dare

  • Kungiyar Irigwe Development Association ta ce ‘yan bindiga sun kashe mata mutane 18 a Ancha
  • Mai magana da yawun bakin kungiyar, Davidson Malison ya zargi Fulani da wannan danyen aikin
  • Kakakin kungiyar MACBAN, Muhammad Nuru Abdullahi ya yi tir da harin, kuma ya wanke Fulani

Plateau - Kungiyar Irigwe Development Association ta koka kan kisan mutanenta da ta ce an yi a kauyen Ancha, yankin Miango a karamar hukumar Bassa.

Rahoton da muka samu a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2021 shi ne an kashe mutum 18 a Ancha a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kasar Rigwe.

Mai magana da yawun bakin kungiyar Irigwe Development Association, Mr. Davidson Malison ya aikawa jaridar Vanguard jawabin da suka fitar bayan harin.

Kara karanta wannan

Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

A jawabin na Davidson Malison, ya ce da kimanin karfe 12:00 na daren ranar Talata ne ‘yan bindiga suka duro kauyen Ancha, suka yi mummunan ta’adi.

Bayan mutane 18 da aka hallaka a harin, wasu mutane shida su na fama da rauni a halin yanzu.

Gwamnan Filato
Gwamna Simon Bako Lalong Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Babu ruwan Fulani inji MACBAN

Ko da ana zargin Fulani ne suka yi wannan aikin, kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN ta karyata wannan zargin.

Shugaban kungiyar MACBAN na reshen jihar Filato, Muhammad Nuru Abdullahi, ya fitar da na su jawabin inda ya tabbatar da kisa da kone-konen da aka yi.

Muhammad Nuru Abdullahi yace sun yi tir da wannan hari da aka kai, tare da Allah-wadai da zargin da aka jefi mutanen Fulani da shi ba tare da hujja ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan daba sun wanke jigon APC da wasu mutane da ruwan 'Acid' a Adamawa

Operation Safe Haven tayi magana

Shi ma kakakin dakarun sojojin na Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa ya tabbatar da harin, ba tare da ya fadi adadin mutanen da aka hallaka ba.

Ishaku Takwa yace sojojin kasa sun kai dauki zuwa kauyen da abin ya wakana, ko da isarsu, sai suka iske cewa ‘yan bindigan sun ruguza gidaje, sun yi gaba.

Shi ma Mai girma Simon Lalong ya yi tir da harin, ya bukaci a kai wa yankin agajin gaggawa.

Barawon waya ya shiga hannu

A makon da ya gabata aka ji yadda Rundunar ‘yan sanda ta jihar Yobe ta kama wani matashi mai suna Usman Ali wanda ya gawurta wurin satar wayoyin mutane.

Mai magana da yawun 'yan sandan Yobe, ASP Dungus Abdulkarim yace Dakarun Crack Squad Unit sun cafke Ali a Nayinawa Sallake bayan sun samu kira a waya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng