BUA, Dangote, Lafarge sun yi alkawarin rage farashin Siminti don gina wasu gidaje, FG

BUA, Dangote, Lafarge sun yi alkawarin rage farashin Siminti don gina wasu gidaje, FG

Gwamnatin tarayya ta yi shirin gina wasu gidaje 300,000 don sayarwa yan Najeriya a farashi mai rahusa
  • Farashin siminti a Najeriya kawo yanzu na tsakanin N3,500 - N4,600 a jihohin Najeriya daban-daban
  • Magina sun yi korafi bisa farashin siminti wanda ya shafi farashin bulo kuma yasa kudin gida yayi tashin gwauron zabo

Birnin Abuja - Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa manyan kamfnonin Siminiti uku; Dangote, Lafarge da BUA sun yi ittifakin rage farashin Siminti a fadin Najeriya.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun matakin Shugaban kasa, Laolu Akande ya saki, a cewar Nairametrics.

Akande yace rage farashin Siminti zai taimakawa gwamnatin tarayya wajen cimma manufarta na samar da gidaje masu sauki da rahusa.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace wani shugaban kwastam mai ritaya a gonarsa a Kwara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BUA, Dangote, Lafarge sun yi alkawarin rage farashin Siminti don gina wasu gidaje, FG
BUA, Dangote, Lafarge sun yi alkawarin rage farashin Siminti don gina wasu gidaje, FG
Asali: Facebook

Akande ya yi maganan ne game da shirin gine-ginen gidaje na gwamnati (ESP) wanda wani shiri ne da aka fitar don rage radadin annobar COVID-19.

Akande yace gwamnati zata gina gidaje 300,000 a karkashin wannan shiri.

A cewarsa:

"Asusun lamunin Family Homes ke gudanar da Shirin ESP, wanda kamfani ne karkashin ma'aikatar kudi, inda gwamnati zata kai kudi."
"Sun gina gidaje sama da 8000 a jihar Borno. Gwamnati kuma ta tattauna manyan kamfanonin siminti uku, Dangote, Lafarge da BUA su sayar da Siminti da rahusa kuma sun amince."

Ya kara da cewa gwamnatocin jihohi 22 sun yi alkawarin bada filaye don ginin gidajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng